Ministan Abuja ya kira taron tsaro na gaggawa

Ministan Abuja ya kira taron tsaro na gaggawa

- Mohammed Bello, ministan babban birnin tarayya, Abuja ya kira taron tsaro na gaggawa

- Mahalarta taron sun hada da shugabannin kananan hukumomi, shugabannin addini, masu sarautun gargajiya, shugbannin kungiyoyi da hukumomin tsaro

- Ministan ya ce an kira taron ne don bitan abubuwan firgici da suka faru a Abuja sakamakon zanga zanga da nufin tabbatar da zaman lafiya da tsaro

Ministan babban birnin tarayya Abuja, Mohammed Bello a ranar Laraba ya kira taron tsaro na gaggawa a kan zanga zangar EndSARS kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Da duminsa: 'Yan sanda sun kama wanda ake zargi da sata a banki a Legas

Ministan Abuja ya kira taron tsaro na gaggawa
Ministan Abuja Mohammed Bello. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Ministan a jawabinsa na bude taro ya ce an kira taron ne, "Don bita kan abubuwan firgici da suka faru cikin mako daya da ya gabata" da nufin tabbatar da ganin lamura sun koma yadda suke a baya a Abuja.

Ya bukaci shugabannin kananan hukumomi, shugabannin addini, masu sarautun gargajiya, shugbannin kungiyoyi da hukumomin tsaro su hada kai don kiyayye rayuka, dukiyoyi tare da tabbatar da cewa an samu zaman lafiya a babban birnin tarayya.

KU KARANTA: 'Yan daba sun mamaye fadar Sarkin Legas, sun kwace sandar ikonsa

"Babban abinda muka sa a gaba tsare rayuka, dukiyoyi da kiyayye al'umma. Don haka mun kira wannan taron ne don tabbatar da an samu zaman lafiya kuma kada a bari abinda ya faru ya sake faruwa," in ji shi.

A wani labarin, Shugaban Kasar Ghana, Nana Akufo-Addo, ya yi kira ga Shugaba Buhari da yin sulhu da masu zanga-zangar #ENDSARS.

Ya yi gargadin cewa rikici bashi zai kawo karshen matsalar zanga zangar da ake don nuna bacin rai kan muguntar yan sanda.

Akufo-Addo ya ce ya yi magana da Shugaba Buhari kan matsalar kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Laraba 21 ga watan Oktoba.

Shugaban na Ghana ya cewa shugaba Buhari a shirye yake don yin sulhu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel