Gwamna Wike ya saka dokar hana fita a wasu kananan hukumomi

Gwamna Wike ya saka dokar hana fita a wasu kananan hukumomi

- An saka dokar hana fita a wasu sassa na jihar Rivers da ke Kudu maso Kudancin Najeriya

- Gwamna Wike da ya sanar da dokar ya ce hakan ya zama dole ne duba da yadda 'yan daba suke yi kutse cikin zanga zangar EndSARS a jihar

- An saka dokar ne a karamar hukumar Oyigbo da wasu sassan kananan hukumomin Obio-Akpor da Fatawal

Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers ya bayyana cewa an saka dokar ta baci awa 24 a wasu daga cikin kananan hukumomin jihar saboda yadda ƴan tada kayar baya suke kawo ruɗani a zanga zangar #ENDSARS a jahar.

Dokar za ta yi aiki ne a kananan hukomomin Oyigbo da kuma wani bangare na kananan hukumomin Obio-Akpor da Port Harcourt.

Gwamna Wike na saka dokar hana fita a wasu kananan hukumomi
Nyesom Wike. Hoto daga Nyesom Ezenwo Wike CON
Asali: Facebook

Wannan yana kunshe cikin wata takarda mai dauke da sa hannun gwamnan wanda mai magana da yawun gwamnan, Kelvin Ebiri ya fitar a ranar Laraba 21 ga Oktoba.

DUBA WANNAN: Da duminsa: 'Yan sanda sun kama wanda ake zargi da sata a banki a Legas

Jaridar Legit.ng ta rawaito cewa Gwamna Wike yayi taron manema labarai sannan ya sanar da dokar ta baci a wasu yankuna ciki akwai karamar hukumar Oyigbo ta jihar.

Ya kuma bayyana cewa an tsawaita dokar zuwa yankunan Mile 1, Mile 2, Emenike, Ikowu da kuma yankin Iloaubuchi na karamar hukumar Port Harcourt a jihar.

KU KARANTA: 'Yan daba sun mamaye fadar Sarkin Legas, sun kwace sandar ikonsa

Gwamnan ya ce sanya dokar ya zama dole ganin yadda yan tawaye suka kawo cikas ga zanga zangar #ENDSARS.

Gwamna Wike ya bayyana cewa wasu daga cikin ɓata gari sun lalata ofishin 'yan sanda da kotuna a karamar hukumar Oyigbo.

A wani labarin, shugaban Kasar Ghana, Nana Akufo-Addo, ya yi kira ga Shugaba Buhari da yin sulhu da masu zanga-zangar #ENDSARS.

Ya yi gargadin cewa rikici bashi zai kawo karshen matsalar zanga zangar da ake don nuna bacin rai kan muguntar yan sanda.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel