Harbi a Lekki: Osinbajo ya magantu, ya bayyana matakin da FG za ta dauka

Harbi a Lekki: Osinbajo ya magantu, ya bayyana matakin da FG za ta dauka

- Farfesa Yemi Osinbajo, mataimakin shugaban kasan Najeriya ya jajanta wa wadanda kashe-kashen Lekki ya shafa

- Ya tabbatar da cewa zuciyarsa tana tare da duk wadanda suka rasa rayukansu a dukkan sassan kasar nan

- Ya bukaci jama'a da su dauka hakuri kuma za a tabbatar da cewa an bi hakkin dukkan wadanda suka rasa rayukansu

Mataimakin shugaban kasar Najerya, Farfesa Yemi Osinbajo, ya nuna damuwarsa a kan harbe-harbe da kashe-kashen 'yan Najeriya da aka yi sakamakon bukatar kawo karshen cin zarafin 'yan sanda da suka yi a kasar nan.

Ya bayyana hakan a wata wallafa da yayi a shafinsa na Twitter a ranar Laraba, The Punch ta tabbatar.

Mataimakin shugaban kasar wanda yace ya samu zantawa da wasu wadanda aka kwantar a asbitoci, ya ce wadanda aka harba ko aka kashe sakamakon zanga-zangar za a tabbatar da an bi musu hakkinsu.

Osinbajo ya ce, "Zuciyata tana tare da wadanda aka harba a Lekki da kuma 'yan sanda ko jami'an tsaron da suka rasa rayukansu a kwanaki kalilan da suka gabata a jihar Legas da sauran jihohi a fadin kasar na.

"Na samu zantawa da wasu da ke asibiti. Fushin aukuwar wadannan lamurran muna ganinsu a tare da mu kuma wasu rashe-rashen ba a iya mayar da su. Amma za mu tabbatar da cewa an bi wa kowa hakkinsa.

“Ina tare da legas da dukkan jihohin da suke fuskantar wannan matsalar a wannan lokacin jarabawar. Muna addu'ar wannan lamarin ba zai sake aukuwa ba. Allah ya albarkaci kowa."

KU KARANTA: ABU-ASUU ta yi watsi da bukatar FG, za ta cigaba da yajin aiki

Harbi a Lekki: Osinbajo ya magantu, ya bayyana matakin da FG za ta dauka
Harbi a Lekki: Osinbajo ya magantu, ya bayyana matakin da FG za ta dauka. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Za mu cigaba da matsanta wa masu laifin da ke barazana ga tsaron kasa - FG

A wani labari na daban, Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya IGP Mohammed Adamu, ya bada umarnin janye dukkan 'yan sandan da ke tsaron lafiyar manyan mutane a fadin kasar nan.

Kamar yadda aka gano, wannan hukuncin ya biyo bayan bukatar sake assasa dokar dakile zanga-zangar EndSARS a tituna.

Wannan umarnin na kunshe ne a wani sako da aka mika ga dukkan kwamandojin 'yan sandan kasar nan a ranar Litinin wanda jaridar The Cable ta gani.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel