Da duminsa: Bata-gari sun fara fashi har cikin gida, sun balle Shoprite a Legas

Da duminsa: Bata-gari sun fara fashi har cikin gida, sun balle Shoprite a Legas

- Jama'ar yankin Surulere da ke jihar Legas sun koka da yadda 'yan daba suka dinga balle gidajensu suna shiga

- Mutane biyu a yankin sun tabbatar da cewa, 'yan daban sun shiga inda suka yi musu fashi da makami

- An gano cewa, hatta babban shagon saide-saide basu bari ba na Shoprite, sun balle inda suka diba kaya masu tarin yawa

Wasu matasa da ake zargin 'yan daba ne sun afka gidajen jama'a inda suka dinga ballesu a yankin Surulere da ke jihar Legas.

A kalla mazauna yankin biyu ne suka tabbatar wa da jaridar The Cable ta wayar salula.

"Tabbas da gaske ne 'yan fashi suna kawo mana hari yanzu. Sun ballo cikin gidajenmu," daya daga cikin jama'ar ya sanar yayin da ake jin harbin bindiga.

A ranar Laraba, jihar Legas ta fuskanci hauhawar rikici inda 'yan daba suka dinga bankawa manyan wurare da ofisoshin 'yan sanda wuta.

Manyan kantuna da wuraren saide-saide ba a kyalesu ba a fadin jihar.

Jaridar The Cable ta gano cewa matasan sun fada babban kantin Shoprite da ke yankin.

Amma kuma rundunar jami'an tsaro da ta hada da 'yan sanda da sojoji sun fatattaki 'yan ta'addan a yankin kuma zaman lafiya ya dawo.

Tun da rana, 'yan daban sun dinga balle shaguna a yankin Lekki da Ajah inda suka dinga musu fashi da makami sannan suna banka musu wuta.

KU KARANTA: Za mu cigaba da matsanta wa masu laifin da ke barazana ga tsaron kasa - FG

Da duminsa: Bata-gari sun fara fashi har cikin gida, sun balle Shoprite a Legas
Da duminsa: Bata-gari sun fara fashi har cikin gida, sun balle Shoprite a Legas. Hoto daga @TheCable
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: IGP ya janye 'yan sanda masu tsaron dukkan manyan mutane a Najeriya

Awani labari na daban, bayan tayar da tarzomar rushe SARS a jihohin da dama na kasar nan, Kwamanda janar na NSCDC, Abdullahi Gana Muhammadu, ya yi kiran gaggawa a kan ma'aikatun gwamnati.

Ya umarci duk wasu kwamandojin kasar nan da su tura jami'ansu don bayar da kariya ga duk wasu ma'aikatu da dukiyoyin da ke kusa da su don gudun asara da kuma lalacewar al'amuran gwamnati.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel