Da duminsa: Fusatattun matasa sun kwace jirgin saman 'yan sanda

Da duminsa: Fusatattun matasa sun kwace jirgin saman 'yan sanda

- Fusatattun jama'a mazauna yankin Oluku da ke kusa da babban birnin jihar Edo sun kwace jirgin saman 'yan sandan Najeriya

- Mazauna yankin sun zagaye jirgin saman tun bayan saukarsa inda suka yi tsammanin an tura shi leken asiri ne

- Amma kuma, an gano cewa jirgin saman ya yi makuwa ne inda ya sauka a wani katon fili da ke kusa da Benin City

Mazauna Oluku kusa da Benin, babban birnin jihar Edo sun kwace jirgin sama na 'yan sandan Najeriya bayan ya manta hanya ya sauka bisa kuskure a yankin.

Mazauna Oluku, wadanda da gaggawa suka zagaye jirgin saman sun yi ikirarin cewa leken asiri aka turo shi kuma sun yi mamakin me ya kai musu jirgin saman'yan sandan yankin a wannan lokacin.

An kasa samun kakakin rundunar 'yan sandan jihar Edo, Child Nwabuzor a lokacin rubuta wannan rahoton, The Nation ta wallafa.

A ranar Laraba, garuruwa da dama sun fuskanci rikici mai tsanani inda 'yan daba suka dinga banka wa kayayyakin gwamnati wuta.

KU KARANTA: Za mu cigaba da matsanta wa masu laifin da ke barazana ga tsaron kasa - FG

Da duminsa: Fusatattun matasa sun kwace jirgin saman 'yan sanda
Da duminsa: Fusatattun matasa sun kwace jirgin saman 'yan sanda. Hoto daga @TheNation
Asali: Twitter

KU KARANTA: ABU-ASUU ta yi watsi da bukatar FG, za ta cigaba da yajin aiki

A wani labari na daban, Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya IGP Mohammed Adamu, ya bada umarnin janye dukkan 'yan sandan da ke tsaron lafiyar manyan mutane a fadin kasar nan.

Kamar yadda aka gano, wannan hukuncin ya biyo bayan bukatar sake assasa dokar dakile zanga-zangar EndSARS a tituna.

Wannan umarnin na kunshe ne a wani sako da aka mika ga dukkan kwamandojin 'yan sandan kasar nan a ranar Litinin wanda jaridar The Cable ta gani.

A umarnin, wanda zai fara aiki a take, gidajen gwamnati, shugaban majalisar dattawa da kuma kakakin majalisar wakilai ne aka tsame.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel