Shugaba Muhammadu Buhari ya yi sabon nadi

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi sabon nadi

- Shugaba Buhari ya nada Sanata Oladipo Olusoga Odujinrin a matsayin shugaban rikon kwarya a hukumar kula da AIDS (NACA)

- An nada Oladipo Olusoga Odujinrin na wa'addin shekaru hudu a karon farko kuma nadin zai fara aiki ranar 6 ga watan Oktoba

- Senator Oladipo Olusoga Odujinrin, kwararren lauya, dan siyasa kuma manazarci, ya hidimtawa Najeriya nan a fanni da yawa

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin Sanata Oladipo Olusoga Odujinrin, MFR, a matsayin shugaban wucin gadi na kwamitin masu bada shawarwari a hukumar kula da yaduwar kanjamau, NACA, na shekaru hudu.

Nadin zai fara aiki daga ranar 6 ga watan Oktoban 2020 kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Shugaba Buhari ya yi sabon nadi
Shugaba Muhammadu Buhari. Hoto daga @TheNationNews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Da duminsa: 'Yan sanda sun kama wanda ake zargi da sata a banki a Legas

Kafin naɗin nasa, Senator Odujinrin ya taba zama daya daga cikin mambobin hukumar a shekarar 2018.

Ya kuma taba riƙe muƙaddashin shugaban hukumar lokacin da aka nada shugabar hukumar Dame Pauline Tallen a matsayin minista a Najeriya.

Odujinrin wanda ya kammala digirinsa na farko a jami'ar Lagos inda ya karanta bangaren shari'a ya kuma samu digirinsa na biyu shima a fannin shari'ar a Jami'ar Havard Law School a kasar Amurka.

KU KARANTA: 'Yan daba sun mamaye fadar Sarkin Legas, sun kwace sandar ikonsa

Ƙwararren lauya, dan siyasa kuma manazarci, Senator Oladipo Olusoga Odujinrin ya bautawa kasar nan a fanni da yawa.

Ya rike mukamin sanata a shekarar 1983. Daga nan ya cigaba da rike mukaman gwamnati da dama ciki har da zama shugaban kamfanin inshora na kasa (1967-68), shugaban kwalejin Nasarawa daga watan Afrilu 2013 zuwa 2015.

Kuma ya taba riƙe mukamin shugaban kungiyar masu sarrafa robobi ta kasa (APMIN) da kuma zama daya daga cikin kwamitin amintattu na asibitin koyarwa na jami'ar Obafemi Awalowo daga shekarar 2005 zuwa 2007.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel