Rikicin #EndSARS: Jerin wurare 23 da bata gari suka kai hari ko bankawa wuta
Cikin sa'o'i 24 kacal, abinda ya fara daga zanga-zangan lumana tsawon kwanaki 12 da suka gabata ya yi munin da yayi sanadiyar lalata ofishoshin gwamnati da na masu zaman kansu.
Abin ya fara muni ne lokacin da wasu bata gari a Abuja, Legas da Edo suka fara kaiwa masu zanga-zanga ba gaira ba dalili.
Masu sharhi lan lamuran yau da kullun sunyi zargin yan siyasa da tura bata garin.
Bude wutan da Sojoji suka yiwa matasan a Lekki Toll gate wanda yayi sanadiyar mutuwan matasa da dama ya karawa wutar mai a jihar Legas.
Fushin haka ya sa wasu matasa suka fara kai hare-hare ofishohin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.

Asali: UGC
DUBA NAN: Bata gari sun sake bankawa gidan jarida mallakin Tinubu, The Nation, wuta
Ga jerin wuraren da aka kaiwa hari:
1. Hukumar kula da tashan jirgin ruwa - An banka wuta
2. Ofishin yan sandan Orile - An banka wuta
3. Garajin Lekki - An banka wuta
4. Tashar Motar BRT dake Oyingbo - An bankawa sabbin motoci wuta
5. Gidan talabijin TVC, Ketu Legas - An banka wuta
6. Ofishin VIO, Ofishin FRSC, Ojodu - An banka wuta
7. Tashar wutan BRT, Ojodu Legas - An banka wuta
8. Tashar BRT dake Berger - An banka wuta
9. Gidan talabijin jihar Legas,Agidingbi, Ikeja - An banka wuta
10. Wajen shakatawa, Oregun, Legas - Agidingbi, Ikeja
11. Fadar Sarkin Legas - An banka wuta
12. Gidan mahaifiyar gwamnan Legas Surulere Legas - An banka wuta
13 Makarantar Kings College
14. Oriental Hotel, Victoria Island Lagos
KU KARANTA: Kisan Lekki: Sarkin Musulmi ya umurci Musulmai su yiwa Najeriya addu'a na musamman ranar Juma'a
15. Sassan bankin AccessBank - An banka wuta
16. Sassan bankin GTBank - An banka wuta
17. Sakatariyan karamar hukumar Ajeromi
18. Sakatariyar karamar hukumar Lagos Island
19. Sakatariyar karamar hukumar Lagos Island East
20. Sakatariyar karamar hukumar Lagos Mainland
21. Sakatariya Ibeju Lekki LCDA
22. Gidan babban yayan gwamnan Legas dake Lagos Island
23. Gidan jaridar The Nation
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng