Yanzu-yanzu: Bata gari sun sake bankawa gidan jarida mallakin Tinubu, The Nation, wuta
- Fusatattun matasa da bata gari sun cigaba da kai hare-hare kamfanoni a jihar Legas
- Bayan bankawa gidan talabijin TVC wuta, sun garzaya gidan jaridar The Nation
- Harbin matasa masu zanga-zanga da Sojoji suka yi ya tayar da wannan tarzoman
Wasu bata gari sun bankawa hedkwatar gidan jaridar The Nation, mallakin babban jigon APC, Asiwaju Bola Tinubu, wuta.
Yanzu haka ginin kamfanin dake Matori a jihar Legas na ci da wuta, a cewar rahoton The Cable
Hakan ya biyo bayan kona gidan talabijin na TVC, duka mallakin dan siyasan.
Ana kyautata zaton cewa ana kai wadannan hare-haren dukiyoyin Bola Tinubu don manufa ta siyasa.

Asali: UGC
DUBA NAN: Kwana hudu bayan harbinsa, babban dan siyasa a Kogi, Adejo, ya mutu
Mun kawo muku rahoton cewa matasan jihar Legas sun afka gidan talabijin TVC News wanda ake zargin mallakin tsohon gwamnan Legas, Asiwaju Bola Tinubu, ne.
Bidiyon da daya daga cikin ma'aikatan kamfanin jaridar ta saki, Precious Amayo, ya nuna yadda wadanda ke cikin shiri suka gudu daga studiyo ana tsakiyan shirin YourView.
Hakazalika bidiyon Arise TV ya nuna yadda gidan jaridan ke ci bal-bal
KU KARANTA: Kisan Lekki: Sarkin Musulmi ya umurci Musulmai su yiwa Najeriya addu'a na musamman ranar Juma'a
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng