Kisan Lekki: Sarkin Musulmi ya umurci Musulmai su yiwa Najeriya addu'a na musamman ranar Juma'a

Kisan Lekki: Sarkin Musulmi ya umurci Musulmai su yiwa Najeriya addu'a na musamman ranar Juma'a

- Sarkin Musulmi ya yi maganarsa ta farko kan rikicin da ya mamaye Najeriya makon nan

- Sarki wanda shine shugaban NSCIA ya ce babu abinda yafi karfin addu'a

- Sultan ya bukaci Musulman Najeriya su koma ga Allah da addu'a

Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar koli ta shari'ar Musulunci a Najeriya (NSCIA), Alh Muhammad Sa'ad Abubakar, ya alanta ranar Juma'a matsayin ranar addu'a ta musamman ga Najeriya.

Sarkin ya ce umurci Musulman Najeriya su yi addu'a bisa rikicin da yayi sanadiyar asarar rayuka da dukiya a Legas, Benin da wasu jihohi.

Mai Alfarma ya jaddada cewa addu'a da komawa ga Allah kadai ya rage a yiwa kasar nan domin samun zaman lafiya.

KARANTA NAN: Kwana hudu bayan harbinsa, babban dan siyasa a Kogi, Adejo, ya mutu

Kisan Lekki: Sarkin Musulmi ya umurci Musulmai su yiwa Najeriya addu'a na musamman ranar Juma'a
Kisan Lekki: Sarkin Musulmi ya umurci Musulmai su yiwa Najeriya addu'a na musamman ranar Juma'a Credit: @presidency
Asali: UGC

KU KARANTA: Bata gari sun sake bankawa gidan jarida mallakin Tinubu, The Nation, wuta

Sarkin Musulmi a jawabin da ya saki a Abuja ranar Laraba, ya bukaci dukkan Limamai su yi Khuduba kan rikicin dake faruwa a kasar domin kwantar da hankalin mabiya.

Jawabin da Femi Abbas, shugaban kwamitin yada labarai na NSCIA ya rattafa hannu, an bukaci dukkan Musulman Najeriya su hada kai da Limamansu wajen addu'a Allah ya zaunar da kasar nan lafiya.

Yace, duk wanda yayi imani da Allah, babu matsalar da ba zata iya magantuwa da addu'a ba.

Hakazalika Sarkin Musulmi ya bukaci Musulmai yan Najeriya dake kasashen wajen su sa baki wajen addu'a.

Daga cikin abubuwan bayan-bayan da ya faru a yau. wasu mutane da ake zargin 'yan ta'adda ne sun balle babbar kotun Igbosere ta jihar Legas, inda suka yi awon gaba da wasu takardun kotun.

A Bidiyon da The Cable suka wallafa, an ga wadanda ake zargin 'yan ta'addan ne suna fita daga kotun da wasu kayan amfanin kotun.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Online view pixel