Da duminsa: 'Yan daba sun balle babban kotu a Legas, sun kwashe takardun shari'a

Da duminsa: 'Yan daba sun balle babban kotu a Legas, sun kwashe takardun shari'a

- Zanga-zangar rushe SARS na cigaba da kawo tashin hankali da asara iri-iri a jihar Legas, inda wasu 'yan ta'adda suka balle babbar kotun Igbosere dake jihar

- A wani bidiyo da aka wallafa, sun nuna yadda wasu 'yan ta'adda suka balle wata kotu suka fitar da kayan amfanin kotun waje

- A cikin bidiyon, an ga inda wasu samari ke fitar da kujeru, fankoki, takardu da sauran kayan amfanin kotun suna lalata su

KU KARANTA: EndSARS: Buhari ya gana da ministan tsaro tare da shugaban tsaro

Wasu mutane da ake zargin 'yan ta'adda ne sun balle babbar kotun Igbosere ta jihar Legas, inda suka yi awon gaba da wasu takardun kotun.

A Bidiyon da The Cable suka wallafa, an ga wadanda ake zargin 'yan ta'addan ne suna fita daga kotun da wasu kayan amfanin kotun.

A bidiyon, an ga wani matashi sanye da hula da rigar alkalai, rike da wasu takardu a hannunsa.

Wasu daga cikinsu sun dauke kujeru, fankoki da sauran kayan amfanin kotun.

An cigaba da ta'addanci da lalata gine-ginen a cikin jihar Legas

KU KARANTA: Da duminsa: Bata-gari sun bankawa ofishin 'yan sanda wuta, sun kone ababen hawa a Ibadan

Karin bayani na nan tafe...

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel