'Yan daba sun mamaye fadar Sarkin Legas, sun kwace sandar ikonsa

'Yan daba sun mamaye fadar Sarkin Legas, sun kwace sandar ikonsa

- Wasu matasa da ake kyautata zaton 'yan daba ne sun kai hari fadar Sarkin Legas da ke Igi Idugaran

- Matasan sun yi barna sun farfasa motoci, ababen hawa da sauran kayan amfani a fadar sarkin tare da kone-kone

- Fusatattun matasan sun kuma kwace sandan sarautar sarkin na Legas da ake kira 'Opa Ase' yayin harin da suka kai

'Yan daba sun mamaye fadar Sarkin Legas, sun kwace sandar ikonsa
Oba Rilwanu Akiolu. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: EndSARS: An kashe mutum 3, an kone coci da ofishin 'yan sanda a Abuja

A Larabar nan ne 'yan daba suka yi dafifi a fadar Sarkin Legas, Rilwanu Akiolu da ke yankin Iga Idugaran, a birnin Legas, suka farfasa ababen hawa da sauran kayan amfani da dama kamar yadda The Punch ta ruwaito.

A wani bidiyo da ke yawo a kafafen sadarwa, ya nuna 'yan tawayen sun yi awon gaba da sandar sarautar wadda aka fi sani da 'Opa Ase'.

KU KARANTA: EndSARS: IGP ya bada umurnin baza 'yan sandan kwantar da tarzoma a jihohin Najeriya

Wani mazaunin yankin ya shaidawa manema labarai cewa 'yan tawayen da suka cika a fadar, sune dai waɗanda suka cinna wuta a gidan da iyalan gwamna Babajide Sanwo-Olu suke.

"Lokacin da suka tafi kai harin gidan mahaifin Sanwo-Olu, yan sanda sun harbi wasu daga cikin su. Wanda hakan ya fusata su har ta kai sun fara musayar wuta tsakaninsu da ƴan sandan har ta kai sun fi karfin yan sanda.

"Yan sandan, wanda ake alakantawa da ofishin 'yan sanda na Adeniji Adele, sun yi gaggawar guduwa daga inda abun ya faru.

"Fusatattun matasan sun nufi hanyar fadar Oba na Lagos. Suna ikirarin cewa shima ma'aikacin gwamnati ne. Maharan suna kai hari ne a duk wani waje mallakin gwamnati," a cewarsa

A wani labarin, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya shawarci shugaba Muhammadu Buhari da ya yi wa masu zanga-zanga jawabi.

Ya gargadi cewa kada shugaban yayi amfani da karfin hukuma akan masu zanga-zangar #ENDSARS.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel