An kulle ofishin jakadancin kasar Birtaniyya dake Najeriya

An kulle ofishin jakadancin kasar Birtaniyya dake Najeriya

- Bayan Amurka, Birtaniya ta rufe ofishohin diflomasiyyarta sakamakon zanga-zanga

- Zanga-zangar EndSARS ta rincabe kuma an yi asarar rayuka da dukiyoyi

- Har yanzu shugaba Buhari bai yi jawabi kan wutan da aka budewa matasa a Lekki ba

Kasar Birtaniya ta bada umurnin rufe ofishohin jakadancinta dake Najeriya sakamakon rikicin da ya biyo bayan zanga-zangan #EndSARS a fadin tarayya.

Game da jawabin da hukumar ta saki a shafinta na yanar gizo a ranar Laraba, Birtaniya ta bayyana cewa ta rufe ofisoshinta ne saboda kiyaye rayukan ma'aikatanta da masu neman biza.

Jawabin ya ce za'a rufe na tsawon kwanaki biyu, kuma wadanda suke shirin zuwa su fasa.

"Sakamakon zanga-zangan dake faruwa a Najeriya kuma saboda kiyaye rayukan ma'aikata da masu neman biza, zamu kulle ofishohinmu na tsawon sa'o'i 48 akalla," jawabin yace.

"Wadanda suka shirya zuwa yanzu, muna bukatanku su dawo makon gobe, daga ranar 26 ga Oktoba, 2020."

"Muna baku hakuri bisa hakan kuma muna fatan za ku fahimta."

KU KARANTA: Zangazangar #EndSARS: Ba bu hannuna a cikin harbe-harben da aka yi a Lekki - Tinubu

An kulle ofishin jakadancin kasar Birtaniyya dake Najeriya
An kulle ofishin jakadancin kasar Birtaniyya dake Najeriya hOTO: UKin NIgeria
Asali: UGC

A bangare guda, Gwamnatin Amurka tace za ta rufe ofishin jakadancinta dake Legas na kwanaki 2 sakamakon zanga-zangar da aketa yi a jihar.

Ta kuma shawarci 'yan kasar da su tabbatar sun kiyayi wuraren da ake zanga-zangar don gudun matsala.

KARANTA: Harbin masu zanga zanga a Lekki: Gwamna Sanwo-Olu ya roƙi yafiyar ƴan Legas

Duk da dai ofishin jakadancin Najeriya basu nuna wanda suke goyon baya ba akan al'amarin zanga-zangar ta shafinsu na Twitter ba. Sun dai sanar da rufe ofishin nasu dake Legas na tsawon kwanaki 2.

Kamar yadda suka wallafa: "Duk da Zanga-zangar lumana ake yi, wasu sun fara rikitar da al'amarin. Yanzu haka suna harin ofisoshin 'yan sanda."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel