Da duminsa: 'Yan sanda sun kama wanda ake zargi da sata a banki a Legas

Da duminsa: 'Yan sanda sun kama wanda ake zargi da sata a banki a Legas

- 'Yan sanda a jihar Legas sun ce sun yi nasarar kama wani daga cikin 'yan daban da suka yi sata a bankuna

- A daren ranar Talata ne wasu da ake zargin 'yan daba ne suka yi kutse wasu bankuna yayin da ake zanga-zangar EndSARS

- 'Yan sandan sun bayyana cewa sun samu wasu adadin kudade daga hannun wanda suka kama amma ba su fayyace adadin ba

Rundunar 'yan sandan jihar Legas, a ranar Laraba ta ce ta kama daya daga cikin wadanda suka kai hari a wasu bankuna a unguwar Lekki a daren ranar Talata.

The Nation ta ruwaito cewa 'yan sandan sun bayyana cewa sun gano wasu kudade da ba a bayyana adadinsu ba a tare da shi.

KU KARANTA: EndSARS: An kashe mutum 3, an kone coci da ofishin 'yan sanda a Abuja

Da duminsa: 'Yan sanda sun kama wanda ake zargi da sata a banki a Legas
'Yan sandan Najeriya. Hoto: @TheNationNews
Asali: UGC

DUBA WANNAN: EndSARS: Kada ka yi amfani da karfin iko kan masu zanga-zanga - Atiku ga Buhari

A wani labarin da Legit.ng Hausa ta wallafa, Ƴar gidan gwamnan Kano, Fatima Ganduje-Ajimobi ta magantu a kan zanga-zangar #ENDSARS da ake don nuna rashin amincewa da zaluncin 'yan sanda.

A wani rubutu da ta wallafa a shafinta na Instagram ranar Asabar, 17 ga Oktoba, tayi kira ga mutane su mallaki katin zaben su sannan kuma bayan ya kaɗa kuri'arsa ya tabbatar an kirga kuri'ar tasa.

"Kuyi zabe kuma kada ku bar mazabar har sai an ƙirga kuri'arku. Kuyi gangami ku raka kuri'unku," Fatima ta rubuta.

"Ku tsaya kai da fata a wajen tattara sakamako sannan ku tabbatar an ƙirga kuri'arku.

Matasa sune mafiya rinjaye kuma su za su ceto kasar mu Najeriya. (#ENDSARS #ENDOPRESSION #FGA)," ta sake rubutawa.

Anasa bangaren, mijinta Idris Ajimobi ya yi kira ga matasa da su tabbatar sun tanadi katin zabensu don tunkarar babban zaben 2023.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel