Da duminsa: Matasa sun kone gidan iyayen Gwamnan Legas, Sanwo-Olu

Da duminsa: Matasa sun kone gidan iyayen Gwamnan Legas, Sanwo-Olu

- Matasa a jihar Legas sun banka wa gidan iyayen Gwamna sanwo-Olu wuta

- Lamarin ya faru wurin karfe 7:45 na safiyar Laraba, ganau ya tabbatar

- A halin yanzu, jami'an hukumar kwana-kwana sun isa suna kashe gobara

Bata-garin matasa a ranar Laraba sun banka wa gidan iyayen gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, wuta. Gidan yana kan titin Omididun inda suka dinga jifansu da duwatsu.

Gwamna Sanwo-Olu ya saka dokar ta baci ta sa'o'i 24 a jihar sakamakon zanga-zangar EndSARS a ranar Talata.

Daga bisani sojoji sun shiga lamarin, abinda ya kawo mutuwar a kalla mutane 7 wadanda da yawansu matasa ne.

Ganau ba jiyau ba sun sanar da jaridar The Punch cewa an ga daya daga cikin matasan rike da jarkar fetur inda suka jike gidan da shi. Amma makwabta sun hana su sakamakon tsoron kada wutar ta taba su.

Bayan wani lokaci, matasan sun yi nasarar kone gidan kurmus.

Ganau din wanda ya bukaci a boye sunansa ya ce, "Wurin karfe 7:45 na safe, fusatattun matasa sun taru wurin gidan iyaye Sanwo-Olu da ke kan titin Omididun a Lagos Island inda suka dinga jifa tare da fasa gilasai.

"Daya daga cikin matasan ya zuba fetur inda aka hana shi saka wuta saboda tsoron rasa rayuka.

“Amma kuma daga bisani matasan sun taru inda suka kone gidan. A halin yanzu 'yan hukumar kwana-kwana ne ke kashe wutar."

An gano cewa 'yan sandan da ke yankin Adeniji Adele ne suka gaggauta zuwa wurin gobarar domin kwantar da tarzoma.

KU KARANTA: Baturiya ta alakanta kanta da Najeriya, ta ce wannan tsohon ministan kakanta ne

Da duminsa: Bata-gari sun kone gidan iyayen Gwamnan Legas
Da duminsa: Bata-gari sun kone gidan iyayen Gwamnan Legas. Hoto daga @MobilePunch
Asali: UGC

KU KARANTA: OPWS: Dakarun soji sun halaka 'yan bindiga, sun kwace miyagun makamai da kwayoyi

A wani labari na daban, bayan saka dokar ta baci a jihar Legas na sa'o'i 24, an soke dukkan tashi ko saukar jiragen sama a fadin jihar.

Gwamnatin jihar ta sanar da saka dokar ta bacin ta sa'o'i 24 sakamakon yadda zanga-zangar lumanar da matasa suka fara ta koma tarzoma a jihar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an durkusar da dukkan kaiwa da kawowa a babban filin sauka da tashin jiragen sama da ke Legas, sakamakon yadda masu zanga-zangar suka mamaye titin zuwa filin jirgin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel