Yanzu-yanzu: Matasa sun bankawa gidan talabijin mallakin Tinubu, TVC News, wuta

Yanzu-yanzu: Matasa sun bankawa gidan talabijin mallakin Tinubu, TVC News, wuta

- Fusatattun matasa sun fara kai hari kamfanoni mallakin jigogin siyasa a Legas

- Bayan bankuna da aka fasa jiya, an banka wuta gidan jaridan TVC

- Har yanzu babu bayani kan halin da ma'aikatan gidan talabijin ke ciki

Labarin da ke shigo mana da duminsa na nuna cewa matasan jihar Legas sun afka gidan talabijin TVC News wanda ake zargin mallakin tsohon gwamnan Legas, Asiwaju Bola Tinubu, ne.

Yanzu-yanzu: Matasa sun bankawa gidan talabijin mallakin Tinubu, TVC News, wuta
Yanzu-yanzu: Matasa sun bankawa gidan talabijin mallakin Tinubu, Hoto: TVC News
Asali: UGC

Bidiyon da daya daga cikin ma'aikatan kamfanin jaridar ta saki, Precious Amayo, ya nuna yadda wadanda ke cikin shiri suka gudu daga studiyo ana tsakiyan shirin YourView.

Hakazalika bidiyon Arise TV ya nuna yadda gidan jaridan ke ci bal-bal

Kalli bidiyon:

KU KARANTA: An kulle ofishin jakadancin kasar Birtaniyya dake Najeriya

A bangare guda, babban sifeton rundunar 'yan sanda (IGP), Mohammed Adamu, a ranar Talata, ya bayyana cewa an kama mutane 12 da ake zzargin da hannunsu a kai hari tare da kone wani ofishin 'yan sanda a Benin, jihar Edo.

A cikin wani jawabi da kakakin rundunar 'yan sanda na kasa (FPRO), Mista Frank Mba, ya fitar, ya bayyana cewa an samu bindigu kirar AK47 guda biyar da aka sace daga ofishin da aka lalata.

DUBA NAN: Ofishin jakadancin Amurka ya rufe ayyukansa a Najeriya

IGP Adamu ya bada umarnin gaggauta tura yan sandan kwantar da tarzoma don kula da rayuka da kuma kula da dukiyoyin gwamnati da na jama'a a fadin kasar nan.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ya fitar ranar Talata yace shugaban yan sandan ya kuma yi umarni da a tura yan sanda masu yawan gaske zuwa ga cibiyoyin kula da masu laifi da ke fadin Kasar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Online view pixel