Baturiya ta alakanta kanta da Najeriya, ta ce wannan tsohon ministan kakanta ne

Baturiya ta alakanta kanta da Najeriya, ta ce wannan tsohon ministan kakanta ne

- Wata mata baturiya mai suna Jessie Joe Jacobs ta bar 'yan kafafen sada zumuntar zamani cike da mamaki bayan ta bayyana cewa Moses Majekodunmi ne kakanta

- A yayin da ta wallafa tsohon hotonsa, ta ce ya ziyarci JF Kennedy tare da Alhaji Abubakar Tafawa Balewa

- Da yawa daga cikin masu tsokacin sun yaba wa kakanta a kan babbar rawar da ya taka wurin habaka bangaren lafiya na kasar nan

Wata baturiya mai suna Jessie Joe Jacobs ta ce Dr Moses Majekodunmi, tsohon ministan Najeriya shine kakanta.

Ta wallafa hoton tuna baya a yayin da kakanta da Firayim minista, Alhaji Tafaawa Balewa suka ziyarci JF Kennedy a 1961.

Matar ta ce tana matukar alfahari da tsatsonta kuma tana alfahari da kakanta baki ne.

Ta kara da cewa, bata taba sanin cewa tana da tsatson bakake ba har sai da ta fara girma. Jessie ta ce ta yi matukar jin dadi bayan da ta gano tana da alaka da bakar fata.

An samu jama'a masu tarin yawa da suka dinga mata sam barka tare da taya ta murnar samun tsatso mai kyau.

Akwai wadanda suka jinjina wa kakanta a kan irin babbar gudumawar da ya bada a fannin habaka kiwon lafiya a kasar nan.

KU KARANTA: OPWS: Dakarun soji sun halaka 'yan bindiga, sun kwace miyagun makamai da kwayoyi

Baturiya ta alakanta kanta da Najeriya, ta ce wannan tsohon ministan kakanta ne
Baturiya ta alakanta kanta da Najeriya, ta ce wannan tsohon ministan kakanta ne. Hoto daga LinkedIn/Jessie Joe Jacob
Asali: UGC

KU KARANTA: Da duminsa: An soke dukkan sauka ko tashin jiragen sama a jihar Legas

A wani labari na daban, Lai Mohammed, ministan al'adu da labari, ya umarci 'yan siyasa, malaman addini, shugabannin gargajiya da kuma duk masu fadi a ji da su daina zuga masu zanga-zangar rushe SARS.

Mohammed ya yi wannan jan kunnen ne a wani taro da NAN ta shirya a ranar Litinin, The Cable ta wallafa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel