EndSARS: Kada ka yi amfani da karfin iko kan masu zanga-zanga - Atiku ga Buhari

EndSARS: Kada ka yi amfani da karfin iko kan masu zanga-zanga - Atiku ga Buhari

- Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya shawarci Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa masu zanga-zanga shawara

- Atiku Abubakar ya ce bai dace shugaban kasa ya yi amfani da karfin ikonsa a kan matasan inda ya ce yanzu lokaci ne na tunani

- Tsohon dan takarar shugaban kasar ya ce amfani da karfin ikon ba zai haifar da alheri ba sai dai rudani da tashin hankali

ENDSARS:kada kayi amfani da karfin iko, bayani ya kamata kayiwa masu zanga zanga.- sakon Atiku ga Buhari
Atiku Abubakar. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya shawarci shugaba Muhammadu Buhari da ya yi wa masu zanga-zanga jawabi.

Ya gargadi cewa kada shugaban yayi amfani da karfin hukuma akan masu zanga-zangar #ENDSARS.

Dan takarar jam'iyyar PDP a zaben shugaban kasa daya gabata ya wallafa hakan ne a shafinsa na Tuwita ranar Talata.

DUBA WANNAN: EndSARS: IGP ya bada umurnin baza 'yan sandan kwantar da tarzoma a jihohin Najeriya

Ya wallafa maganar ne sa'o'i kadan bayan umarnin da shugaban yan sanda, Adamu Mohammed ya bayar na tura jami'an kwantar da tarzoma a kowane sashe na kasar nan.

Ya wallafa, "banji dadin rasa rayukan da akayi ba, da kuma yadda yan ta'adda suke lalata masu zanga zangar lumana ta #ENDSARS.

"Roko na ga gwamnatin shugaba Buhari shine kada yayi kuskuren amfani da jami'an tsaro akan masu zanga zangar #ENDSARS.

KU KARANTA: EndSARS: An kashe mutum 3, an kone coci da ofishin 'yan sanda a Abuja

"Masu zanga-zangar nan suna da dalili da kuma manufa.

"Yanzu lokaci ne da ya kamata ace an saurare su kuma an biya musu bukatunsu

"Amfani da jami'an tsaro bazai kawo mafita ba sai dai rudani.

"Idan gwamnati ta nuna damuwa yan kasa zasu rusuna, yanzu lokaci ne na yin tunani, bawai amfani da karfin iko ba.

"A saboda haka, ina mai kira ga shugaban kasa da ya yi wa yan kasa musamman matasa jawabi."

A wani labarin daban, Ƴar gidan gwamnan Kano, Fatima Ganduje-Ajimobi ta magantu a kan zanga-zangar #ENDSARS da ake don nuna rashin amincewa da zaluncin 'yan sanda.

A wani rubutu data wallafa a shafinta na Instagram ranar Asabar, 17 ga Oktoba, tayi kira ga mutane su mallaki katin zaben su sannan kuma bayan ya kaɗa kuri'arsa ya tabbatar an kirga kuri'ar tasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel