Za mu cigaba da matsanta wa masu laifin da ke barazana ga tsaron kasa - FG

Za mu cigaba da matsanta wa masu laifin da ke barazana ga tsaron kasa - FG

- Gwamnatin tarayya ta sanar da shirinta na cigaba da tsananta wa masu laifukan ta'addanci

- Kamar yadda babban sakataren ma'aikatar cikin gida, Shuaibu Belgore ya ce hakan ta zama dole

- Ya sanar da hakan a yayin kaddamar da sabon dakin taro na hukumar kwana-kwana a Abuja

Gwamnatin tarayya za ta cigaba da matsanta wa 'yan ta'adda da masu laifuka da ke barazana ga tsaron cikin gida, Shuaib Belgore, babban sakataren ma'aikatar cikin gida ya sanar da hakan a ranar Talata a ABuja.

Belgore, a jawabinsa na kaddamar da sabon babban dakin taro na hukumar kwana-kwana na tarayya, ya ce za su cigaba da matsantawa domin ganin bayan 'yan ta'adda a fadin kassar nan.

Ya tabbatar wa da FFS cewa ma'aikatar cikin gida a shirye take wurin taimaka wa hukumar kwana-kwana wurin cimma burinsu na tsare rayuka da kadarorin jama'a.

Ya jinjinawa FFS a kan jajircewarsu duk da kuwa babban kalubalen da suke fuskanta na rashin kudi, kayan aiki da kuma rashin isassun ma'aikata da horo, Daily Trust ta wallafa.

"Abin farin cikin shine, a hankali ana cigaba da samar da kayan aiki da kuma ma'aikata masu horo mai kyau.

“Ina kira gareku da ku cigaba da taka rawar da kuka saba takawa wurin kashe gobara da kuma yakar annoba tare da tseratar da rayukan jama'a," yace.

KU KARANTA: Gwamnonin Najeriya sun bayyana matakai 5 da suke dauka a kan EndSARS

Za mu cigaba da matsanta wa masu laifin da ke barazana ga tsaron kasa - FG
Za mu cigaba da matsanta wa masu laifin da ke barazana ga tsaron kasa - FG. Hoto daga @Dailytrust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: An soke dukkan sauka ko tashin jiragen sama a jihar Legas

A wani labari na daban, rundunar soji ta Operation Whirl Stroke ta samu nasarar halaka wasu 'yan bindiga, kwato miyagun makamai da kuma wasu kwayoyi a jihar Benue.

A sakamakon cigaban kokarin dakarun sojin Najeriya na ganin bayan 'yan bindiga da sauran miyagun al'amura a fadin kasar nan, rundunar Operation Whirl Stroke ta halaka 'yan bindiga biyu a jihar Nasarawa.

Rundunar hadin guiwa ta fita sintiri a ranar 18 ga watan Oktoban 2020 a kauyukan Kango da Adumata inda ta tarar da wasu 'yan bindiga.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel