ABU-ASUU ta yi watsi da bukatar FG, za ta cigaba da yajin aiki

ABU-ASUU ta yi watsi da bukatar FG, za ta cigaba da yajin aiki

- Kungiyar ASUU reshen jami'ar Ahmadu Bello ta yi watsi da bukatar gwamnatin tarayya

- Kamar yadda kungiyar ta bayyana, ba za ta koma aiki ba har sai FG ta fara cika alkawarinta

- ASUU da gwamnatin tarayya za su shiga taro a yau domin jin ta matsayar kungiyar

Kungiyar malamai masu koyarwa ta jami'o'i (ASUU), reshen jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, ta dauka alwashin cigaba da yajin aikinta sannan ta yi watsi da bukatar gwamnatin tarayya ga kungiyar.

A ranar Juma'a ta makon da ya gabata ne gwamnatin tarayya ta bukaci aiki da kungiyar domin samun hanyar samar da kudi isasshe tare da cika alkawarin da ta daukar mata a 2013.

Hakazalika, ministan kwadago da aikin yi, Chris Ngige, ya ce babban akantan kasar nan zai fara sakin kudi a ranar ko kafin 6 ga watan Nuwamba na alawus din mambobin kungiyar, yayin da wata biliyan 30 za ta fara fitowa daga watan Mayun 2021 zuwa Fabrairun 2022

Amma kuma, a tron da ASUU reshen ABU suka yi, sun ce za su janye yajin aikin ne bayan gwamnatin tarayya ta fara biya musu bukatunsu, Daily Trust ta wallafa.

KU KARANTA: Da duminsa: Sojoji da 'yan sanda sun mamaye yankin filin jirgin sama a Abuja

ABU-ASUU ta yi watsi da bukatar FG, za ta cigaba da yajin aiki
ABU-ASUU ta yi watsi da bukatar FG, za ta cigaba da yajin aiki. Hoto daga @Dailytrust
Asali: Twitter

KU KARANTA: EndSARS: Lai Mohammed ya aike wa shugabannin addinai sako mai muhimmanci

Awani labari na daban, bayan saka dokar ta baci a jihar Legas na sa'o'i 24, an soke dukkan tashi ko saukar jiragen sama a fadin jihar.

Gwamnatin jihar ta sanar da saka dokar ta bacin ta sa'o'i 24 sakamakon yadda zanga-zangar lumanar da matasa suka fara ta koma tarzoma a jihar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an durkusar da dukkan kaiwa da kawowa a babban filin sauka da tashin jiragen sama da ke Legas, sakamakon yadda masu zanga-zangar suka mamaye titin zuwa filin jirgin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel