EndSARS: An kashe mutum 3, an kone coci da ofishin 'yan sanda a Abuja

EndSARS: An kashe mutum 3, an kone coci da ofishin 'yan sanda a Abuja

- An kashe mutum uku sakamakon hare-haren da 'yan daba ke kai wa masu zanga-zanga a Abuja

- Ana kyautata zaton 'yan daban sun kuma kone wani coci da gidan mai a babban birnin tarayya, Abuja

- Har ila yau, 'yan daban dauke da makamai sun banka wa wani coci wuta a Dutse Makaranta a Abuja

Akalla mutum uku ake kyautata zaton an kashe tare da jikkata wasu da dama a Dutse Alhaji dake Abuja, yayin da ƴan banga ke ci gaba da barnata dukiyoyi a babban birnin tarayya Abuja.

Ana zargin ƴan bangar da cinnawa ofishin yan sanda dake yankin Dutse Makaranta wuta.

An kuma yi barna a wata coci da kuma gidan mai kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Sun lalata ababen hawa da shaguna da dama a yankin.

EndSARS: An kashe mutum uku, an kone coci da ofishin 'yan sanda a Abuja
Yan sandan Najeriya. Hoto daga @PulseNigeria247
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: ENDSARS: Ku tanadi katin zabe, ku tabbatar kun kaɗa kuri'un ku - Fatima Ganduje

Ƴan bangar, wanda mazauna yankin suka gani da idonsu, sunzo ne a motocin akori kura da manyan motoci, maharan sun kai hari ga masu zanga zangar #ENDSARS tun satin daya gabata.

A wancan satin sun kashe wani dan zanga zangar mai suna Tony Onome a yankin Kubwa.

A ranar Litinin ma sun lalata wasu shaguna wanda suke a rufe saboda zanga zangar a yankin Apo.

Sun kona motoci da shaguna, tare da kai hari kan duk wanda suka gani.

KU KARANTA: A kan tattaro min takardun neman aiki a kalla 200 duk lokacin da na tafi ziyarar aiki - Pantami

Mutum bakwai ne suka mutu a hadarin,kamar yadda yan sanda suka tabbatar.

Masu zanga zanga sun mamaye titunan Abuja a kokarin da suke na ganin an biya musu bukatar su.

Yawan kai harin da yan daba keyi ne yasa masu zanga zangar ke zama cikin rukuni don zama cikin shirin tunkarar kowanne irin hari.

A halin yanzu dai ana iya cewa yan daban suna yawo a tituna don tada hankali a babban birnin Kasar nan,kuma suna kai hari wurare mabambanta.

Masu zanga zangar na zargin gwamnati da daukar nauyin yan ta'addan don dakatar dasu daga fafutukar da suke.

Wanda basa goyon bayan zanga zangar suna ganin cewa abin da yake faruwa yan ta'adda ne da masu kin jinin gwamnati ke shiryawa don nunawa mutane gazawar gwamnati.

A wani labarin, Shugaban yan sandan Najeriya, Muhammad Adamu ya bada umarnin tura yan sandan kwantar da tarzoma don kula da rayuka da kuma kula da dukiyoyin gwamnati dana jama'a a fadin Kasar nan.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ya fitar ranar Talata yace shugaban yan sandan ya kuma yi umarni da a tura yan sanda masu yawan gaske ga cibiyoyin kula da masu laifi a fadin Kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel