EndSARS: Gwamnatin Ekiti ta kulle makarantun jihar na mako daya

EndSARS: Gwamnatin Ekiti ta kulle makarantun jihar na mako daya

- Zanga-zangar EndSARS ta canza zani a jihohi daban-daban na fadin tarayya

- Gwamnatocin jiha sun fara sanya dokar han fita domin kwantar da tarzoma

- Bata gari sun kwace zanga-zangar daga hannun ainihin masu na lumana inda suka fara kona ma'aikatun gwamnati

Gwamnatin jihar Ekiti ta bada umurinn kulle dukkan makarantu masu zaman kansu da na gwamnati na tsawon mako daya sakamakon canza zanin da zanga-zangar #EndSARS tayi.

Kwamishanan Ilimin jihar, Dr Kofoworola Aderiye, ya bada umurinn ranar Litinin a matsayin matakin kare rayukan dalibai, malamai, da sauran ma'aikatan makarantu dake fuskantar matsala yayin zuwa makaranta.

A jawabin da mai yada labaran ma'aikatar ilimin jihar, Abiobola Dada, ya sake, ya ce ba za'a koma karatu ba sai ranar Litinin, 26 ga Oktoba, 2020.

Za ku tuna cewa masu zanga-zangar EndSARS sun daburta lissafin dalibai da malaman makarantan da suka koma karatu ranar Litinin.

Sakamakon toshe hanyoyin da suka yi, sai da dalibai suka tafiya mai tsawo a kafa.

DUBA NAN: Gwamnatin Buhari za ta nemi bashin $11bn don gina layin dogon Legas-Calabar

EndSARS: Gwamnatin Ekiti ta kulle makarantun jihar na mako daya
EndSARS: Gwamnatin Ekiti ta kulle makarantun jihar na mako daya Credit: @chanellstv
Asali: Twitter

KARANTA: Buhari ya nada Sanusi Garba sabon shugaban hukumar kula da wutan lantarki a Najeriya

A wani labarin, bayan saka dokar ta baci a jihar Legas na sa'o'i 24, an soke dukkan tashi ko saukar jiragen sama a fadin jihar.

Gwamnatin jihar ta sanar da saka dokar ta bacin ta sa'o'i 24 sakamakon yadda zanga-zangar lumanar da matasa suka fara ta koma tarzoma a jihar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an durkusar da dukkan kaiwa da kawowa a babban filin sauka da tashin jiragen sama da ke Legas, sakamakon yadda masu zanga-zangar suka mamaye titin zuwa filin jirgin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel