EndSARS: IGP ya bada umurnin baza 'yan sandan kwantar da tarzoma a jihohin Najeriya

EndSARS: IGP ya bada umurnin baza 'yan sandan kwantar da tarzoma a jihohin Najeriya

- Babban Sufetan Ƴan Sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya bada umurnin tura rundunar kwantar da tarzoma jihohin kasar

- Shugaban ƴan sandan ya bada umurnin ne biyo bayan rikice-rikicen da suka barke a wasu sassan kasar biyo bayan zanga-zangar EndSARs

- A jihohi da dama an samu rasa rayuka, dukiyoyi da kai hare-haren ga hukumomin gwamnati

Shugaban yan sandan Najeriya, Mahmud Adamu, ya bada umarnin tura yan sandan kwantar da tarzoma don kula da rayuka da kuma kula da dukiyoyin gwamnati dana jama'a a fadin Kasar nan.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ya fitar ranar Talata yace shugaban yan sandan ya kuma yi umarni da a tura yan sanda masu yawan gaske ga cibiyoyin kula da masu laifi a fadin Kasar.

DUBA WANNAN: A kan tattaro min takardun neman aiki a kalla 200 duk lokacin da na tafi ziyarar aiki - Pantami

EndSARS: IGP ya bada umurnin baza 'yan sandan kwantar da tarzoma a jihohin Najeriya
'Yan sandan Najeriya. Hoto daga @PulseNigeria247
Asali: Twitter

Umarnin na zuwa ne biyo bayan karuwar tarwatsa tare da fasa kayayyakin gwamnati dana ɗai ɗaikun mutane da yake faruwa a jihohin kasar dama birnin tarayya Abuja.

"Bugu da kari, kwamishinonin yan sanda a jihohi 36 na Najeriya dama birnin tarayya Abuja, za su yi aiki don gano tare da ware ɓata gari daga cikin masu zanga zangar lumana; za a kama masu barna tare da ladabtar dasu dasu a wureren da ya dace.

KU KARANTA: ENDSARS: Ku tanadi katin zabe, ku tabbatar kun kaɗa kuri'un ku - Fatima Ganduje

"Shugaban yan sandan yace sun kama mutane 12 da ake zargi da kai hari da farfasa kayayyaki a wani ofishin yan sanda a Benin, jihar Edo. An kuma ƙwato bindigun AK47 guda biyar da aka sace a ofishin yan sandan da aka kai harin.

"Shugaban na yan sanda ya kuma yi kira ga al'umma da su taimakawa rundunar da muhimamman bayanai da zasu basu damar cafke wanda suka gudu daga gidajen yari.

"Ya kuma shawarci iyaye dasu saka ido akan 'ya'yansu don ganin cewa basu sabawa doka ba, ya kuma kara da cewa rundunar zata cigaba da kare dukiya da rayukan ƴan kasa," a cewar sanarwa.

A wani labarin daban, Wasu da ake zargin 'yan daba ne sun kone wasu gine-gine a cikin sakatariyar karamar hukumar Ajeromi na jihar Legas.

Sakataren watsa labarai na karamar hukumar, Sheriff Fakanle ya tabbatarwa wakilin The Punch afkuwar lamarin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel