Legas: 'Yan daba sun banka wa sakatariya wuta, anyi sace-sace

Legas: 'Yan daba sun banka wa sakatariya wuta, anyi sace-sace

- 'Yan daba dauke da makamai sun afka sakatariyar karamar hukumar Ajeromi na jihar Legas

- 'Yan daban suna ta shiga ofisoshi suna sace kaya sannan wasu na kone gine-gine da motocci

- Sakataren watsa labarai na karamar hukumar, Sheriff Fakanle ya tabbatar da afkuwar lamarin

Legas: 'Yan daba sun banka wa sakateriya wuta, sun sace kayayyaki a Legas
Legas: 'Yan daba sun banka wa sakateriya wuta, sun sace kayayyaki a Legas. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

Wasu da ake zargin 'yan daba ne sun kone wasu gine-gine a cikin sakatariyar karamar hukumar Ajeromi na jihar Legas.

Sakataren watsa labarai na karamar hukumar, Sheriff Fakanle ya tabbatarwa wakilin The Punch afkuwar lamarin.

Da aka tuntube shi misalin karfe 1.13 na rana, Fakunle ya ce ana cigaba da kai harin a sakatariyar karamar hukumar.

DUBA WANNAN: A kan tattaro min takardun neman aiki a kalla 200 duk lokacin da na tafi ziyarar aiki - Pantami

Ya ce, "A halin yanzu da na ke magana da kai, 'yan daba dauke da makamai sun afka sakatariyar karamar hukuma ta. An lalata kayayyaki na miliyoyin naira. Wasu daga cikin 'yan daban suna shiga ofisoshin mu, sun awon gaba da kayayyaki. An kone gine-gine da motoci, matasa na sata a cikin sakatariyar."

Tunda farko, wasu matasa da ake zargin 'yan daba ne sun kai hari ofishin 'yan sanda da ke karamar hukumar Ifelodun sun banka masa wuta.

KU KARANTA: ENDSARS: Ku tanadi katin zabe, ku tabbatar kun kaɗa kuri'un ku - Fatima Ganduje

Kazalika wasu da ake zargin bata gari ne sun kona ofishin 'yan sanda da ke Orile Iganmu duk a jihar Legas.

A wani labarin daban, Funke Egbemode, kwamishinan watsa labarai na jihar Osun, ta ce harin da aka kai wa gwamnan jihar Gboyega Oyetola a wurin zanga-zangar #EndSARS a Osogbo, babban birnin jihar, yunkuri ne na neman kashe shi.

Oyetola yana tsaka da yi wa masu zanga-zangar jawabi a mahaɗar Olaiya a Osogbo, babban birnin jihar, inda wasu da ake zargin ƴan-daba ne suka ƙaddamar da hari a kan taron jama'ar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel