Yanzu-yanzu: Buhari ya nada Sanusi Garba sabon shugaban hukumar kula da wutan lantarki a Najeriya
- Majalisar dattawa ta yi zaman majalisa ranar Talata duk da rikicin zanga-zangan dake faruwa a kasar
- Majalisar ta karbi sakon shugaba Buhari kan sabon shugaban hukumar NERC da ya zaba
- Daga cikin wadanda ya zaba akwai maza biyu da mace daya
Shugaba Muhammadu Buhari ya zabi wadanda yake son a nada sabbin shugabannin hukumar lura da wutar lantarki a Najeriya watau NERC.
Shugaban kasar ya aike da sunayensu majalisar dokokin tarayya domin tabbatar da su.
Shugaban majalisar dattawa, Ahmed Ibrahim Lawan, ya karanta wasikar da Buhari ya aiko musu a zauren majalisa ranar Talata, 20 ga watan Oktoba, 2020.
Wadanda Buhari ya zaba sune:
1 . Engr. Sanusi Garba - Shugaba
2. Musiliu Olalekan Oseni - Mataimakin shugaba
3. Aisha Mahmud - Kwamishana
Bayan haka, Buhari ya aike da da sunan Chief Onyenuchi Nnamani, wakilin yankin kudu maso yamma, matsayin daya daga cikin mambobin hukumar kula da lamuran yan sanda watau Police Service Commision PSC.

Asali: Twitter
KU KARANTA: Gwamnatin Buhari za ta nemi bashin $11bn don gina layin dogon Legas-Calabar
DUBA NAN: An hanawa wani Likita Musulmi hakkin zama dan kasa saboda ya ki musafaha da mace
A bangare guda, majalisar dattawa, a ranar Talata ta yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa 'yan Najeriya jawabi nan take a kan zanga-zangar da matasa ke yi a jihohin kasar game da cin zali da 'yan sanda ke yi da kuma neman kawo gyara a gwamnati.
Majalisar ta kuma bukaci jami'an 'yan sanda su bawa matasa da ke zanga-zangar ta EndSARS kariya daga 'yan daba da ke neman mamaye zanga-zangar kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Majalisar ta cimma wannan matsayar ne bayan wani takarda da Sanata Biodun Olujimi ya gabatar mai taken "EndSARS: Bukatar yin garambawul mai sahihanci."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng