Ta faru ta kare: Rundunar 'yan sanda ta haramta zanga zanga a fadin jihar Legas

Ta faru ta kare: Rundunar 'yan sanda ta haramta zanga zanga a fadin jihar Legas

- Rundunar 'yan sanda ta haramta duk wani nau'in tarurruka ko zanga zanga a fadin jihar Lagos daga ranar Talata 20 ga watan Oktoba

- Haka zalika, rundunar ta tabbatar da cewa, masu zanga zangar #EndSARS sun kona ofishin rundunar na Orile, jihar Lagos tare da jikkata jami'an ta

- Rundunar ta kuma ce ba za ta lamunci tashin hankula a jihar ba, ganin yadda aka samu gurbatattu a cikin masu zanga zangar

Sakamakon kai hare hare ga jami'an 'yan sanda da fararen hula, gwamnati ta kakaba dokar ta baci ta awanni 24 a jihar Legas, rundunar 'yan sandan Legas ta haramta zanga zanga a fadin jihar.

Rundunar 'yan sanda ta sanar da hakan a wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata ta hannun jami'in hulda da jama'a na rundunar, SP Olumuyiwa Adejobi.

KARANTA WANNAN: Sabuwar zanga zanga ta barke a Abuja: An kashe mutum daya, da yawa sun jikkata

Ta faru ta kare: Rundunar 'yan sanda ta haramta zanga zanga a fadin jihar Legas
Ta faru ta kare: Rundunar 'yan sanda ta haramta zanga zanga a fadin jihar Legas - ThisDayLive
Asali: UGC

Sanarwar ta ce: "Rundunar 'yan sandan jihar Legas na sanar da al'uma cewa da su kauracewa yin taro ko zanga zanga, akan kowanne irin dalili, an haramta yin hakan a fadin jihar Legas."

"Sakamakon hakan, an rarraba jami'an tsaro zuwa lungu da sakunan jihar domin tabbatar da jama'a sun bin wannan doka sau da kafa."

KARANTA WANNAN: DSS ta gayyaci wani babban malamin addinin Kirista kan rikicin Jos

Rundunar 'yan sandan ta kuma tabbatar da cewa masu zanga zanga sun kona ofishin rundunar na Orile da misalin karfe 10 na safiyar ranar Talata.

Sanarwar ta ce "Jami'an mu sun samu manyan raunuka, inda har muke samun jita jitar cewa daya daga cikinsu ya mutu," kamar yadda jaridar This Day Live ta wallafa.

Rundunar ta kara da cewa, "Ta tabbata cewa an samu gurbatattun a cikin masu zanga zangar #EndSARS, rundunar 'yan sandan jihar ba zata lamunci duk wani farmaki ko aikin ta'addanci ba.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa jami'an tsaro za su kare hakkokin bil Adama da demokaraddiyar kasa.

Ya kuma zama dole al'umar jihar su bi umurnin da aka sanya na dokar ta baci a jihar, bijirewa hakan zai tilasta cafkesu da yanke masu hukunci.

A wani labarin, Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi a ranar Litinin ya ce gwamnatin jihar ba za ta lamunci kai cin zarafin da jami'an 'yan sanda ke yiwa al'umar jihar ba.

Mr Umahi, wanda ya bayyana hakan a babban dakin taro na tsohon gidan gwamnatin jihar yayin ganawa da masu zanga zangar #EndSARS, ya ce ba zai lamunce tsare tituna a ko ina a jihar ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel