EndSARS: Majalisa ta bukaci Buhari ya yi wa 'yan Najeriya jawabi

EndSARS: Majalisa ta bukaci Buhari ya yi wa 'yan Najeriya jawabi

- Majalisar Dattawa ta Najeriya ta bukaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gaggauta yi wa 'yan kasa jawabi kan zanga-zangar EndSARS

- Majalisar ta kuma yi kira ga rundunar 'yan sanda ta bawa matasa da ke zanga-zangan lumana kariya daga bata gari da ke kai musu hari

- Majalisar ta kuma shawarci Shugaban kasa ya kafa kwamiti da ta kunshi manyan mutane da matasa ke girmamawa don bincike kan jami'an SARS

Majalisar Dattawa, a ranar Talata ta yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa 'yan Najeriya jawabi nan take a kan zanga-zangar da matasa ke yi a jihohin kasar game da cin zali da 'yan sanda ke yi da kuma neman kawo gyara a gwamnati.

Majalisar ta kuma bukaci jami'an 'yan sanda su bawa matasa da ke zanga-zangar ta EndSARS kariya daga 'yan daba da ke neman mamaye zanga-zangar kamar yadda The Punch ta ruwaito.

DUBA WANNAN: A kan tattaro min takardun neman aiki a kalla 200 duk lokacin da na tafi ziyarar aiki - Pantami

EndSARS: Majalisa ta bukaci Buhari ya yi wa 'yan Najeriya jawabi
Shugaba Buhari da Majalisar Dattawa. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

Majalisar ta cimma wannan matsayar ne bayan wani takarda da Sanata Biodun Olujimi ya gabatar mai taken "EndSARS: Bukatar yin garambawul mai sahihanci."

Majalisar ta cimma wannan matsayar ne bayan wani takarda da Sanata Biodun Olujimi ya gabatar mai taken "EndSARS: Bukatar yin garambawul mai sahihanci."

KU KARANTA: ENDSARS: Ku tanadi katin zabe, ku tabbatar kun kaɗa kuri'un ku - Fatima Ganduje

Har wa yau, majalisar ta shawarci masu zanga-zanga su koma gidajensu su bawa gwamnati lokaci domin ta yi aiki a kan bukatun da suka gabatar.

Yan majalisar na tarayya sun kuma bukaci Buhari ya kafa kwamitin shari'a da ta kunshi 'yan Najeriya masu kima da mutunci da matasa za su girmama domin gano azzaluman jami'an SARS a kama su a bincike su.

A wani labarin, Wasu da ake zargin 'yan daba ne sun kona ofishin 'yan sanda da ke Apapa Iganmu a jihar Legas kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Lamarin ya faru ne misalin karfe 9.45 na safiya a cewar wani da abin ya faru a idonsa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel