Za mu tona asirin 'yan daban da ke basaja a matsayin makiyaya a Kudu - Miyetti Allah

Za mu tona asirin 'yan daban da ke basaja a matsayin makiyaya a Kudu - Miyetti Allah

- Kungiyar makiyaya Fulani ta ce za ta tona asirin wadanda ke aikata laifi a kudu suna fakewa da sunanta

- Kungiyar ta bayyana hakan ne wurin wani taron wayar wa juna kai da ta shirya a jihar Enugu

- Miyetti Allah ta ce akwai wasu 'yan ta'adda a yankin na kudu maso gabas da ke aikata laifuka sna fake wa da sunanta

Za mu tona asirin 'yan daban da ke basaja a matsayin makiyaya a Kudu - Miyetti Allah
Makiyaya. Hoto daga @Vanguardnewngr
Asali: Twitter

Kungiyar makiyaya ta Meyetti Allah (MACBAN) ta bayyana aniyarta ta sake duba irin barnar da 'yan ta'adda suka yi a yankin kudu maso gabas wanda tace suna fakewa da Fulani.

Shugaban kungiyar reshen kudu maso gabas, Alhaji Gidado Siddiki ne ya bayyana haka a ranar Talata a garin Enugu kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Saddiki yace shirin nasu sunyi shi ne musamman don samar da kyakkwawar alaka da fahimtar juna tsakanin Fulani da kuma mazauna yankin.

DUB WANNAN: A kan tattaro min takardun neman aiki a kalla 200 duk lokacin da na tafi ziyarar aiki - Pantami

Ya kuma ce kungiyar tasu ta hori mambobinta akan yadda zasu kyautata alaka da mutanen da suke zaune dasu a yankunan da suke, dama yadda zasu kula da dokokin gwamnati.

"Muna jin dadin yadda gwamnati da al'umma a nan yankin kudu maso gabas suke bamu goyon baya da kuma kyautata alaka da makiyaya.

"Zamu tabbatar cewa munci gaba da tsabtace harkar kiwo don samar da ingantattun kayayyaki ga mazauna yankin," Siddiki ya bayyana.

Siddiki ya kuma ce kungiyar tana fafutukar yadda zata dakatar da yara masu kananan shekaru zuwa yawon kiwo, tare da hukunta duk wanda aka kama da laifin.

"Wannan zai nisanta kungiyar MACBAN daga zargin laifukan ta'addanci da ake zarginta da aikatawa ga ƴan ba ruwana.

DUBA: ENDSARS: Ku tanadi katin zabe, ku tabbatar kun kaɗa kuri'un ku - Fatima Ganduje

"Ƴayan mu kamata ya yi ace an basu karfin gwiwa don suje makaranta, bawai a barsu suyi ta yawon korar shanu ba, kuma idan hakan ya zama dole to ya kasance suna tare da wani babban da zai kula da motsinsu," inji shi.

Yace kungiyar ta kuma haramta kiwon dare saboda yana bawa bata gari damar lalata gonaki da sauran kayayyakin amfani.

Siddiki ya bayyana cewa MACBAN ta dauki alhakin bin duk wata hanya don karfafa alaka tsakanin Arewa da kudu maso gabas.

"Zamu ci gaba da nuna irin yadda ake bamu kulawa duk kuwa da irin bambancin al'adu dake tsakaninmu", inji Saddiki.

A wani labarain daban, Shugaban yan sandan Najeriya, ya bada umarnin tura yan sandan kwantar da tarzoma don kula da rayuka da kuma kula da dukiyoyin gwamnati dana jama'a a fadin Kasar nan.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ya fitar ranar Talata yace shugaban yan sandan ya kuma yi umarni da a tura yan sanda masu yawan gaske ga cibiyoyin kula da masu laifi a fadin Kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel