Da duminsa: An sake ƙona wani ofishin 'yan sanda a Legas (Bidiyo)

Da duminsa: An sake ƙona wani ofishin 'yan sanda a Legas (Bidiyo)

- Wasu da ake kyautata zaton 'yan daba ne sun kona ofishin rundunar 'yan sanda da ke Ifelodun a jihar Legas

- Wannan na zuwa ne bayan wasu 'yan daban sun kona wani ofishin na 'yan sanda da ke Oriile Iganmu duk dai a Legas

- Wasu da abin ya faru a idonsu sun ce 'yan daban sun kai wa ofishin 'yan sandan hari ne bisa zargin 'yan sandan sun harbi wasu matasa

Wasu da ake zargin 'yan daba ne sun kona ofishin 'yan sanda da ke karamar hukumar Ifelodun na jihar Legas.

Wasu da lamarin ya faru a gabansu sun tabbatar wa The Punch afkuwar abin a ranar Talata.

Tunda farko, wasu da ake kyautata zaton bata garin ne sun kona ofishin yan sanda da ke Orile Iganmu duk dai a jihar ta Legas.

Lamarin ya faru ne misalin karfe 9.45 na safiya kamar yadda wadanda abin ya faru a gabansu suka bayyana.

KU KARANTA: ENDSARS: Ku tanadi katin zabe, ku tabbatar kun kaɗa kuri'un ku - Fatima Ganduje

Da duminsa: An sake kona wani ofishin 'yan sanda a Legas
Ofishin 'yan sanda a Legas. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: A kan tattaro min takardun neman aiki a kalla 200 duk lokacin da na tafi ziyarar aiki - Pantami

An kuma ruwaito cewa an kai wa ofishin 'yan sanda da ke Pako hari.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa wasu 'yan daban sun kai hari a ofishin 'yan sanda da ke Ajeromi amma 'yan sanda sun dakile harin.

Ya ce, "Rikicin ya fara ne a Orile Iganmu. Mutane suna zanga-zanga ta lumana sai 'yan sanda suka harbe su, yaran sun ji cewa 'yan sanda sun kashe mutanensu a Iganmu, sun kuma kone ofishin 'yan sanda ta Layeni.

"Hankulan mutane ya tashi. Mun kai mutane takwas asibiti. Sun samu munanan raunuka."

Da aka tuntube shi, Sakataren watsa labarai na karamar hukumar Ajeromi Ifelodun, Sheriff Fakunle ya ce, "Eh, da gaske an kona ofishin 'yan sanda na Layeni. Lamarin ya faru misalin karfe 11 na safe.

"'Yan sandan sun fatattaki 'yan daban a ofishinsu na Ajeromi."

A wani labarin daban, Funke Egbemode, kwamishinan watsa labarai na jihar Osun, ta ce harin da aka kai wa gwamnan jihar Gboyega Oyetola a wurin zanga-zangar #EndSARS a Osogbo, babban birnin jihar, yunkuri ne na neman kashe shi.

Oyetola yana tsaka da yi wa masu zanga-zangar jawabi a mahaɗar Olaiya a Osogbo, babban birnin jihar, inda wasu da ake zargin ƴan-daba ne suka ƙaddamar da hari a kan taron jama'ar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel