Yanzu-yanzu: An saka dokar hana fita -ba dare, ba rana- a jihar Legas
- Bayan kwanaki 12, gwamnatin Legas ta bi sahun Edo wajen sanya dokar ta baci
- An kona ofishin yan sanda dake Orile da safiyar Talata a Legas
- Gwamnan ya baiwa ma'aikata sa'o'i uku su koma gidajensu zuwa karfe 4 na rana
Labarin da ke shigo mana da duminsa na nuna cewa sakamakon zanga-zanga, kashe-kashe da kone-konen dake faruwa a jihar Legas, gwamnatin jihar ta saka dokar ta baci a dukkan sassan jihar.
Gwamnan jihar, Babajide Sanwo-Olu ya bayyana hakan a shafinsa na Tuwita, ranar Talata.
Ya baiwa mutanen jihar daman komawa gidajen daga yanzu zuwa karfe 4 saboda daga lokacin ba''a son ganin kowa a waje.
"Na zuba ido kan yadda zanga-zangan #EndSARS da aka fara cikin lumana ya zama wani abu daban da ka iya cutar da al'ummarmu, " yace
"An rasa rayuka da sassan jiki yayinda wasu bata gari ke cakuda da masu zanga-zanga domin aika-aika a jihar mu."
"A matsayinmu na gwamnati da ta san aikinta kuma ta shirya amsa bukatun #EndSARS, ba zamu zuba ido muna gani ana tayar da tarzoma a jiharmu ba."
"Saboda haka na sanya dokar hana fita na 24hrs a dukkan sassan jihar daga karfe 4 na yau, 20 ga Oktoba, 2020. Ba'a amince a ga kowa ba illa ma'aikata masu muhimmanci."
KU KARANTA: An hanawa wani Likita Musulmi hakkin zama dan kasa saboda ya ki musafaha da mace

Asali: Twitter
DUBA: Ya isa haka, ku sassauta - Tinubu ya yi kira ga masu zanga-zanga
Mun kawo muku cewa, wasu da ake zargin 'yan daba ne sun kona ofishin 'yan sanda da ke Apapa Iganmu a jihar Legas kamar yadda The Punch ta ruwaito.
Lamarin ya faru ne misalin karfe 9.45 na safiya a cewar wani da abin ya faru a idonsa. Mai magana da yawun karamar hukumar Orile-Iganmu, Ayo Micheal ya ce, "Eh, an kai hari ofishin 'yan sandan.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng