EndSARS: Lai Mohammed ya aike wa shugabannin addinai sako mai muhimmanci

EndSARS: Lai Mohammed ya aike wa shugabannin addinai sako mai muhimmanci

- Ministan al'adu da labari, Lai Mohammed, ya shawarci shugabannin al'umma su saka baki akan zanga-zangar da matasa ke yi akan rushe SARS

- Mohammed ya fadi hakan ne a wani taro da NAN ta shirya a ranar Litinin, yace zanga-zangar ta riga ta canja salo, matasa sun koma kone-kone da kashe-kashe a garuruwa

- Yanzu haka, masu zanga-zangar sun kona ofishin 'yan sanda dake Ugbekun a jihar Benin, bayan balle gidan gyara hali da suka yi, fursinoni suka gudu

Lai Mohammed, ministan al'adu da labari, ya umarci 'yan siyasa, malaman addini, shugabannin gargajiya da kuma duk masu fadi a ji da su daina zuga masu zanga-zangar rushe SARS.

Mohammed ya yi wannan jan kunnen ne a wani taro da NAN ta shirya a ranar Litinin, The Cable ta wallafa.

Zanga-zangar da suke ta yi na tsawon kwanaki 12, ta samu goyon baya da daukar nauyi na ciki da wajen kasar nan.

Duk da sifeta janar na 'yan sanda, Mohammed Adamu, ya rushe rundunar SARS, amma matasan sun cigaba da zanga-zanga a wurare daban-daban a Najeriya.

A ranar Litinin ne wasu 'yan ta'adda suka balle gidan gyaran hali na Oko da ke layin Benin-Sapele a birnin Benin, a jihar Edo, inda fursunoni da dama suka tsere.

Bayan wasu awanni, an bankawa ofishin 'yan sanda dake Ugbekun a jihar Benin wuta.

Akwai ta'addanci da dama da aka yi a fadin kasar nan.

Mohammed yace idan shugabanni suka cigaba da zurawa matasa ido, to za su cigaba da cin karensu babu babbaka.

Ya kara da cewa, ya ji kunyar yadda wasu shugabanni suka cigaba da tunzura matasan suna yadda suka ga dama a tituna.

Ya kara da cewa, maimakon shugabanni su yi wa al'amarin garanbawul, sun cigaba da yabawa matasa suna ta'addanci, wannan ba zanga-zanga bace, kisa, tada rikici da barnar dukiyoyi da rayuka kawai ake yi.

Ya kamata shugabanni su tabbatar sun sa baki akan wannan al'amarin, don ba zai haifi da mai ido ba.

KU KARANTA: EndSARS: Jama'a sun fusata, yunwa ta yawaita a kasar nan - Gwamnoni

EndSARS: Lai Mohammed ya aike wa shugabannin addinai jan kunne
EndSARS: Lai Mohammed ya aike wa shugabannin addinai jan kunne. Hoto daga @Thecable
Asali: Twitter

KU KARANTA: Rikicin APC na cikin gida: Marafa ya nufi kotun koli a kan taron jam'iyya

A wani labari na daban, ministan tsaro, Bashir Magashi, ya ja kunnen matasan Najeriya akan kada su keta iyakar tsaro sakamakon zanga-zangar rushe SARS duk da gwamnatin tarayya ta fahimci manufarsu.

Magashi yayi wannan kiran ga matasa a wata takarda da kakakin ma'aikatar, Mohammad Abdulkadri ya saki, kamar yadda jaridar Premium times ta ruwaito.

Ma'aikatar ta yi wannan jan kunnen a lokacin da shugaban kamfen din Buhari, Danladi Pasali, ya jagoranci wakilai a ma'aikatar tsaro dake Abuja.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel