Gwamnonin Najeriya sun bayyana matakai 5 da suke dauka a kan EndSARS
- Gwamnonin Najeriya sun ce sun yanke hukuncin cika duk bukatun da masu zanga-zangar EndSARS suka mika musu
- Gwamna Fayemi wanda shine shugaban kungiyar gwamnonin ya yi kira ga masu zanga-zangar da su dakata
- Gwamnan ya kushe harin da aka kai wa takwaransa, Gwamna Oyetola na jihar Osun daga wurin zanga-zangar
Kungiyar gwamnonin Najeriya (NGF) ta ce za ta shawo kan dukkan bukatun da matasan Najeriya masu zanga-zanga a kan cin zarafi da kisan da 'yan sanda suke yi a kasar nan.
Dubban matasan Najeriya sun kwashe kwanaki a kan titunan kasar nan inda suke bukatar a kawo karshen cin zarafin da 'yan sanda na musamman masu yaki da fashi da makami ke yi.
Gwamnatin tarayya tuni ta rushe rundunar kuma ta maye gurinta da wata sabuwa.
Amma kuma har yanzu matasan basu bar kan titunan ba domin suna son ganin matakin da gwamnatin ta dauka.
A wata takarda da gwamnonin Najeriya suka fitar a ranar Litinin, 19 ga watan Oktoba, Gwamna Fayemi na jihar Ekiti ya ce za a shawo kan dukkan bukatun matasan.
1. Kafa kwamitin bincike domin karbar dukkan korafin a kan cin zarafin da jami'an SARS suke yi.
2. Fara biyan diyya ga dukkan wadanda lamarin ya shafa.
3. Karbar bukatar masu zanga-zangar na inganta shugabanci da kuma gujewa take hakki.
4. Daukar mataki a kan dukkan bukatun masu zanga-zangar amma sun nuna damuwarsu a kan yadda bukatun ke sauyawa.
5. Roko a kan a janye zanga-zangar saboda illar da zai yi ga tattalin arziki kuma 'yan daba sun fara shiga lamarin.
KU KARANTA: Filayen sauka da tashin jiragen sama 5 masu matukar kyau a Afrika

Asali: UGC
KU KARANTA: Kwankwaso ya bude gidan rediyo a Kano, ya nada Maude Gwadabe shugaba
A wani labari na daban, rikicin cikin jam'iyyar APC ta jihar Zamfara na cigaba da aukuwa tsakanin bangarorin guda biyu, wanda har kotu bata gama hukunci akai ba, Legit.ng ta wallafa.
Bangare daya na jam'iyyar, wanda Sanata Kabiru Marafa ke jagoranta sun ce za su daukaka kara zuwa kotun koli akan hukuncin da kotun daukaka kara ta Sokoto tayi akan taron jam'iyyar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng