Babur din zinari: Hotunan kasaitattun ababen hawan Shugaba Donald Trump

Babur din zinari: Hotunan kasaitattun ababen hawan Shugaba Donald Trump

- Shugaban kasar Amurka, Donald Trump yana da matukar son kayatattun motoci

- Misali, motarsa kirar Lamborghini Diablo an yi ta tun 1997 yayin da kirar Rolls-Royce wacce yafi so an yi ta a 1956

- Mota kirar Tesla Roadster tana daga cikin tsirarun motocinsa na zamanin nan

A yayin da zaben kasar Amurka na 2020 ke gabatowa, Legit.ng ta tattaro muku jerin motocin alfarma da Shugaba Trump ya mallaka. A gane cewa, wannan jerin motocin an bayyana su a 2017 ne, akwai yuwuwar an kara wasu a kai.

An gano cewa, a 2015 shugaban kasa Trump ya ce arzikinsa ya kai dala biliyan 10. Amma kuma wani rahoton mujalla Fobes bayan shekaru biyu ya nuna cewa arzikinsa ya karye inda ya koma dala biliyan 3.7.

Ga wasu daga cikin motocin da ke garejin Shugaban kasar Amurka.

1. Rolls-Royce Silver Cloud

Babu shakka Trump yana son mota kirar Rolls-Royce da har ya siye ta 1956. Rahotanni sun nuna cewa motar tana daya daga cikin motocin da suka fi soyuwa a zuciyarsa. A kasuwa kudinta zai kai N9.9 zuwa N44.5.

Babur din zinari: Hotunan kasaitattun ababen hawan Shugaba Donald Trump
Babur din zinari: Hotunan kasaitattun ababen hawan Shugaba Donald Trump. Hoto daga Insider
Asali: UGC

2. Lamborghini Diablo

Wannan motar tana nuna yadda Trump ke son abubuwa masu tsada. Tana daya daga cikin motoci fitattu.

Babur din zinari: Hotunan kasaitattun ababen hawan Shugaba Donald Trump
Babur din zinari: Hotunan kasaitattun ababen hawan Shugaba Donald Trump. Hoto daga Insider
Asali: UGC

KU KARANTA: Kwamitin bincike na Salami na kokarin kakaba wa Magu laifi ta kowacce hanya - Lauyan Magu

3. Mercedes-Benz SLR McLaren

An fara yin kirar motar nan a 2003 lokacin da kamfanin Mercedes ke hade da na McLaren.

Babur din zinari: Hotunan kasaitattun ababen hawan Shugaba Donald Trump
Babur din zinari: Hotunan kasaitattun ababen hawan Shugaba Donald Trump. Hoto daga Insider
Asali: UGC

4. Cadillac Allante

A gane cewa, shugaban kasan Amurkan ya mallaki Cardillac ba daga tak ba. Yana da Convertible V8 da Escalade SUV.

Babur din zinari: Hotunan kasaitattun ababen hawan Shugaba Donald Trump
Babur din zinari: Hotunan kasaitattun ababen hawan Shugaba Donald Trump. Hoto daga Insider
Asali: UGC

5. Tesla Roadster

Wannan motar tafi kama da ta 'yan tseren wasan mota kuma tana amfani da wutar lantarki.

KU KARANTA: EndSARS: Jama'a sun fusata, yunwa ta yawaita a kasar nan - Gwamnoni

Babur din zinari: Hotunan kasaitattun ababen hawan Shugaba Donald Trump
Babur din zinari: Hotunan kasaitattun ababen hawan Shugaba Donald Trump. Hoto daga Insider
Asali: UGC

6. 24-karat Gold Chopper

Yana daya daga cikin babura masu jikin zinari. Duk da wannan ba mota bace, an yi ta zinari kuma Paul Teutal Sr.

Babur din zinari: Hotunan kasaitattun ababen hawan Shugaba Donald Trump
Babur din zinari: Hotunan kasaitattun ababen hawan Shugaba Donald Trump. Hoto daga Insider
Asali: UGC

A wani labari na daban, yayin da nahiyar Afrika ta zama babban wurin shakatawa da kuma hada-hada, akwai wasu manyan filayen jiragen sama da nahiyar ke alfahari da su.

A Afrika, akwai filayen sauka da tashin jiragen sama biyar da nahiyar ke alfahari da su wurin kyau da kayatarwa, Pulse.ng ta ruwaito.

An zuba miliyoyin daloli wurin gina filayen sauka da tashin jiragen saman wanda hakan Yasa suka kasance kayatattu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel