An hanawa wani Likita Musulmi hakkin zama dan kasa saboda ya ki musafaha da mace

An hanawa wani Likita Musulmi hakkin zama dan kasa saboda ya ki musafaha da mace

- Allah daya, gari ban-ban: Kin musafaha da mace ya zama abin zargi a kasar Jamus

- Yayinda a wasu kasashe kuma yin hakan abin suka ne da laifi

- Har ila yau ana sukan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kan gaisawa da mata ajnibai

Wata kotun kasar Jamus ta yanke hukuncin hanawa wani Likita Musulmi hakkin zama dan kasa saboda ya ki hannu da hannu da matar dake bashi takardar zama dan kasa.

Likitan wanda asalin dan kasar Lebanon ne ya koma kasar Jamus da zama a 2002 kuma ya kasance bai musafaha da mata saboda dalilai na addini, The Guardian ta ruwaito.

Kotun dake zaune Baden-Württemburg ta yanke cewa dukkan wanda ya ji musafaha saboda "wani ra'ayi na addini ko al'ada" saboda suna ganin mata "a matsayin fitina" basu shirya zama da mutan Jamus ba.

DUBA NAN: Ya isa haka, ku sassauta - Tinubu ya yi kira ga masu zanga-zanga

Bayan shekaru 13 a kasar da kuma cin jarabawar zama dan kasa da maki mai yawa, Likitan na gab da zama dan kasa.

Amma a ranar taron bashi shahadar zama dan kasa da akayi a 2015, yaki musafaha da wata mata kuma hakan ya sa hukumomi suka janye shahadar kuma suka hanashi.

Ya bayyanawa cewa ya yiwa matarsa alkawarin cewa ba zai yi musafaha da wata mata ba.

Bai samu nasara a karar da ya shigar kotun Stuttgart ba kuma ya daukaka kara VGH. Yayinda aka saurari karan, kotun ta ce zai iya sake daukaka kara wata kotun daban.

Alkalin yace musafaha "abune da ya dade cikin rayuwar mutane da al'ada."

Kotun ta ce duk wanda yaki musafaha saboda jinsi ya saba dokar kasar.

An hanawa wani Likita Musulmi hakkin zama dan kasa saboda ya ki musafaha da mace
An hanawa wani Likita Musulmi hakkin zama dan kasa saboda ya ki musafaha da mace Hoto daga Fadar shugaban kasa
Asali: Facebook

KU KARANTA: Nan da makonni biyu daruruwan yan Najeriya zasu kamu da Korona - Gwamnatin tarayya

A bangare guda, gwamnatin kasar Jamus karkashin jagorancin Cansala Angela Merkel ta taimakawa Najeriya da kudi Yuro milyan 26 wanda yayi daidai da bilyan 11.3 a kudin Najeriya.

Ofishin jakadancin kasar Jamus dake nan Najeriya a jawabin da ya saku ya ce an bada gudunmuwar ne domin taimakawa Najeriya wajen yakar cutar Coronavirus da kuma karfafa alaka da kasar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel