Da duminsa: Gwamnatin jihar Legas ta sake rufe makarantu

Da duminsa: Gwamnatin jihar Legas ta sake rufe makarantu

- Gwamnatin jihar Legas ta umarci rufe makarantun kudi da na gwamnati dake jihar sakamakon tayar da tarzomar da masu zanga-zangar rushe SARS suke yi

- Kwamishinan ilimi, Folasade Adefisayo, ta sanar da hakan ne, inda tace don tabbatar da lafiyar dalibai, malamai da iyayensu, wajibi ne a dakatar da makarantun na wani lokaci

- Ta kuma shawarci iyaye da su tabbatar sun sa ido akan yaransu don kada ayi amfani da su wurin tada tarzoma da hankulan jama'a

Gwamnatin jihar Legas ta umarci duk daliban jihar, na makarantar gwamnati da ta kudi, da su zauna a gida saboda tarzomar da masu zanga-zangar rushe SARS suka tayar.

Kwamishinan ilimi ta jihar, Folasade Adefisayo, wacce ta bayar da wannan umarnin, tace don tabbatar da lafiyar dalibai, malamai da kuma iyayen yara, wajibi ne su dakatar da zuwa makarantu a wannan lokacin na tsanani.

Ta kuma shawarci iyaye da su saka ido akan yaransu, don kada ayi amfani da su wurin tayar da hankalin al'umma, The Nation ta wallafa.

Kamar yadda Adefisayo ta ce, jihar Legas zata sanar da lokacin da za'a bude makarantu nan ba da jimawa ba.

KU KARANTA: EndSARS: Ministan tsaro ya aike da jan kunne da kakkausar murya ga masu zanga-zanga

Da duminsa: Gwamnatin jihar Legas ta sake rufe makarantu
Da duminsa: Gwamnatin jihar Legas ta sake rufe makarantu. Hoto daga @TheNation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kwamitin bincike na Salami na kokarin kakaba wa Magu laifi ta kowacce hanya - Lauyan Magu

A wani labari na daban, a ranar Lahadi, Gwamnan jihar Ekiti kuma shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Dr Kayode Fayemi, yace hankalin takwarorinsa a tashe suke akan yunwa, damuwa da kuma tashin hankalin da ke Najeriya.

Fayemi ya bayyana yadda gwamnoni ke a shirye wurin yin aiki tukuru don kawo karshen matsalolin dake tattare da kasar nan.

Gwamnan yayi magana ne a lokacin da yake mika sakon godiyarsa ga mutane a Patrick's Catholic Cathedral a Ado-Ekiti, a cikin al'amuran da ya shirya don murnar cika shekaru 2 a ofishin gwamnati.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel