Bidiyon ragargazar 'yan Boko Haram da sojin sama suka yi a maboyarsu a Borno

Bidiyon ragargazar 'yan Boko Haram da sojin sama suka yi a maboyarsu a Borno

- Rundunar sojin sama na cigaba da samun nasarar ragargazar 'yan Boko Haram da maboyarsu a jihar Borno, inda suka kashesu da dama a karamar hukumar Dikwa

- Kamar yadda rahoto yazo a wata takarda da kakakin rundunar sojin Najeriya, Manjo Janar John Enenche ya saki a ranar 18 ga watan Oktoba 2020, 'yan Boko Haram sun sha kashi a hannun sojojin

- Enenche ya sanar da yadda sojojin sama suka yi amfani da dabaru da salo na musamman wurin gano maboyarsu da ragargazar su wanda yayi sanadiyyar mutuwar 'yan Boko Haram da yawa

Sojojin sama sun kai wa 'yan Boko Haram hari ta jirgin sama a karkashin shirin su na "Operation Lafiya Dole", wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar 'yan Boko Haram da dama.

Kamar yadda wata takarda da kakakin rundunar sojin Najeriya, Manjo Janar John Enenche ya bayyana, harin da sojojin sama suka kai wa 'yan Boko Haram kamar yadda bayanan sirri suka nuna, ya tabbatar da kashe yawancinsu.

Sojojin sun ragargaji 'yan Boko Haram din dake maboyarsu dake Tsilala kusa da Kaza a karamar hukumar Dikwa dake jihar Borno.

An yi harbin saman a ranar 18 ga watan Oktoba 2020, bayan amfani da na'urar da ta nuna wuraren da mafi yawan 'yan Boko Haram din suke.

Mayakan NAF sun yi amfani da jiragen sama na yaki don tabbatar da kai harin wuraren da suka kamata don ragargazar 'yan Boko Haram da maboyarsu.

KU KARANTA: Duba gagarumar motar da Ronaldo ya roka daga wurin fitaccen dan dambe Mayweather

Bidiyon ragargazar 'yan Boko Haram da sojin sama suka yi a maboyarsu a Borno
Bidiyon ragargazar 'yan Boko Haram da sojin sama suka yi a maboyarsu a Borno. Hoto daga @TheNation
Asali: UGC

KU KARANTA: Gwamnati bata da karfin samar wa da jama'a isassun ayyukan yi - Ngige

A wani labari na daban, An dakatar da dalibai 20 'yan aji 4 da ke babbar makarantar sakandire ta Loreto a Zimbabwe sakamakon kamasu da laifin lalata da juna a watan Yuli.

Da yake makarantar ta maza da mata ce, an kama daliban tsirara suna lalata a inda yara matan ke kwana na makarantar da ke Silobela, yayin da suke shirin fara jarabawar watan Yuni zuwa Yuli.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: