EndSARS: Ministan tsaro ya aike da jan kunne da kakkausar murya ga masu zanga-zanga

EndSARS: Ministan tsaro ya aike da jan kunne da kakkausar murya ga masu zanga-zanga

- Ministan tsaro, Bashir Magashi, ya ja kunnen matasa masu zanga-zanga akan SARS da kada su tada tarzoma a Najeriya

- Yace shugaban kasa ya fahimci manufar zanga-zangar tasu, kuma gwamnatin tarayya za ta dage wurin samar musu abinda suke so

- Ya kara da cewa, tunda gwamnati ta gane abinda suke so, to su bada lokaci, domin nan bada jimawa ba za'a dauki matakin da ya dace

Ministan tsaro, Bashir Magashi, ya ja kunnen matasan Najeriya akan kada su keta iyakar tsaro sakamakon zanga-zangar rushe SARS duk da gwamnatin tarayya ta fahimci manufarsu.

Magashi yayi wannan kiran ga matasa a wata takarda da kakakin ma'aikatar, Mohammad Abdulkadri ya saki, kamar yadda jaridar Premium times ta ruwaito.

Ma'aikatar ta yi wannan jan kunnen a lokacin da shugaban kamfen din Buhari, Danladi Pasali, ya jagoranci wakilai a ma'aikatar tsaro dake Abuja.

Ministan ya bayyana shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin shugaba mai nagarta, kuma yayi godiya ga kwamitin kamfen din akan dagewarsu wurin ganin cigaban kasa.

Ya roki masu zanga-zangar da su bai wa gwamnatin tarayya damar yunkurawa wurin ganin tayi abinda suka bukata, su kuma bada lokaci don ganin hakan ya tabbata.

KU KARANTA: Hotuna tare da bayani a kan fitaccen bangon Benin mai kama da bangon duniya na China

EndSARS: Ministan tsaro ya aike da jan kunne da kakkausar murya ga masu zanga-zanga
EndSARS: Ministan tsaro ya aike da jan kunne da kakkausar murya ga masu zanga-zanga. Hoto daga Saharareporters.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Kwamitin bincike na Salami na kokarin kakaba wa Magu laifi ta kowacce hanya - Lauyan Magu

A wani labari na daban, daliban jami'o'i karkashin inuwar kungiyar daliban jami'o'i ta kasa ta ce hakurinsu ya kare sakamakon dogon yajin aikin da kungiyar malamai masu koyarwa na jami'o'i suka fada.

Daliban sun ce za su nuna rashin jin dadinsu a kan yadda yajin aikin ke tsawaita a ranar Talata.

Sun ce za su fara zanga-zangar ne ta gaban katafaren ginin majalisar tarayya sannan su wuce zuwa ofishin ma'aikatar ilimi daga nan su garzarya zuwa ma'aikatar kwadago da aikin yi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel