Da duminsa: Kotu ta fara sauraron ƙara mai ƙalubalantar naɗin sabon Sarkin Zazzau

Da duminsa: Kotu ta fara sauraron ƙara mai ƙalubalantar naɗin sabon Sarkin Zazzau

- Kotu ta fara sauraron karar da Iyan Zazzau, Bashar Aminu ya shigar na kallubalantar nadin Ahmad Bamalli a matsayin Sarkin Zazzau

- A cikin takardar karar, Bashar Aminu ya ce ba a yi adalci ba wurin nada sarkin don shine ya samu kuri'u mafi rinjaye a kuri'ar da masu zaben sarki suka kada

- Kotun ta dage cigaba da sauraron shari'ar har zuwa ranar 27 ga watan Oktoban 2020

Babban kotun jihar Kaduna da ke zamanta a Dogarawa Sabon Gari karkashin jagorancin mai shari'a Kabir Dabo ta fara sauraron karar da aka shigar na kallubalantar nadin da gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ya yi wa Ahmad Bamalli a matsayin Sarkin Zazzau.

An nada Bamalli a matsayin Sarkin Zazzau na 19 ne bayan rasuwar tsohon sarki Alhaji Shehu Idris.

Tunda farko Daily Trust ta ruwaito cewa daya daga cikin wadanda suka nemi kujerar sarautar ta Zazzau, Iyan Zazzau, Bashar Aminu ya shigar da kara kotu.

DUBA WANNAN: Dalibi dan shekara 20 ya auri mata biyu cikin wata daya (Hotuna)

Da duminsa: Kotu ta fara sauraron ƙara mai ƙalubalantar naɗin sabon Sarkin Zazzau
Sarkin Zazzau, Ahmad Bamalli. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

Aminu na daya daga cikin mutane hudu da masu zaben sarki suka mika sunayensu ga gwamnan don zaben daya daga cikinsu da zai nada sarki.

Kuma shine ya samu kuri'u mafi rinjaye a kuri'ar da masu zaben sarkin suka kada.

KU KARANTA: A kan tattaro min takardun neman aiki a kalla 200 duk lokacin da na tafi ziyarar aiki - Pantami

Amma gwamnatin jihar Kaduna ta yi watsi da zaben na su ta bada umurnin a sake sabon zabe.

Jerin sunayen na biyu da aka gabatarwa gwamnatin ya kunshi sunan Bamalli wadda daga bisani aka zabe shi ya zama sarki.

Aminu, cikin karar da ya shigar ya ce ba ayi adalci wurin zaben ba.

Kotun ta dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 27 ga watan Oktoba.

A wani rahoton, Kakakin shugaban kasa, Garba Shehu ya bayyana a ranar Asabar cewa, Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da kafa kwamiti na musamman da rarraba kayan tallafi ga jahohi 12 wanda ambaliyar ta lahanta a fadin kasar nan.

Shugaban ya dauki matakin ne biyo bayan karban bayanin ambaliyar ruwan daya faru a shekarar da muke bankwana da ita.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel