EndSARS: Jama'a sun fusata, yunwa ta yawaita a kasar nan - Gwamnoni

EndSARS: Jama'a sun fusata, yunwa ta yawaita a kasar nan - Gwamnoni

- Gwamnan jihar Ekiti, kuma shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, yace shi da takwarorinsa sun damu da halin da kasa ke ciki

- Yace Najeriya na fama da tashin hankali, rashin tsaro da matsananciyar yunwa, kuma a shirye suke da su yi gyara akai

- Ya fadi hakan yayin da yake mika godiyarsa a cocin Katolika ta Patrick dake Ado-Ekiti, yayin cikarsa shekaru 2 a matsayin gwamnan Ekiti

A ranar Lahadi, Gwamnan jihar Ekiti kuma shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, Dr Kayode Fayemi, yace hankalin takwarorinsa a tashe suke akan yunwa, damuwa da kuma tashin hankalin da ke Najeriya.

Fayemi ya bayyana yadda gwamnoni ke a shirye wurin yin aiki tukuru don kawo karshen matsalolin dake tattare da kasar nan.

Gwamnan yayi magana ne a lokacin da yake mika sakon godiyarsa ga mutane a Patrick's Catholic Cathedral a Ado-Ekiti, a cikin al'amuran da ya shirya don murnar cika shekaru 2 a ofishin gwamnati.

Kuma babban Rabaren, Felix Ajakaye, ya roki masu zanga-zanga da su dakata don ba gwamnatin tarayya damar daukar mataki.

Feyemi yace, "Mutane su na cikin damuwa, bakar yunwa da kuma tashin hankali. A matsayina na mutumin da na dage wurin ganin gwamnatin baya ta gyara al'amuran da suka baci, zan fi fahimtar duk abubuwan da ke faruwa."

"Ni da takwarori na muna cikin damuwa, kuma muna tsaye tsayin-daka wurin ganin anyi gyara akan al'amarin SARS, saboda na lura ita ce babbar matsalar jama'a," a cewarsa.

KU KARANTA: Sirrin da Awolowo ya sanar da ni game da Babangida - Orji Kalu

EndSARS: Jama'a sun fusata, yunwa ta yawaita a kasar nan - Gwamnoni
EndSARS: Jama'a sun fusata, yunwa ta yawaita a kasar nan - Gwamnoni. Hoto daga @MobilePunch, @Dailytrust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kwamitin bincike na Salami na kokarin kakaba wa Magu laifi ta kowacce hanya - Lauyan Magu

A wani labari na daban, daliban jami'o'i karkashin inuwar kungiyar daliban jami'o'i ta kasa ta ce hakurinsu ya kare sakamakon dogon yajin aikin da kungiyar malamai masu koyarwa na jami'o'i suka fada.

Daliban sun ce za su nuna rashin jin dadinsu a kan yadda yajin aikin ke tsawaita a ranar Talata.

Sun ce za su fara zanga-zangar ne ta gaban katafaren ginin majalisar tarayya sannan su wuce zuwa ofishin ma'aikatar ilimi daga nan su garzarya zuwa ma'aikatar kwadago da aikin yi.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel