EndSARS: Mota kirar SUV ta mitsike masu zanga-zanga 4 a kan titi

EndSARS: Mota kirar SUV ta mitsike masu zanga-zanga 4 a kan titi

- Wata mota kirar SUV ta murkushe rayuka hudu tare da raunata wasu hudun a jihar Edo

- Hakan ya faru ne da wasu masu zanga-zangar EndSARS a jihar da ke kan tituna

- Lamarin ya faru a titin First East Circular da ke Benin City yayin da suke niyyar hada wuta

A kalla mutum 4 ne suka rasa ransu sakamakon mugun hatsarin da suka hadu da shi yayin zanga-zangar EndSARS a jihar Edo.

Wata mota kirar SUV ce da ta tunkaro titin da gudu ta halaka su kuma ta bar wasu da miyagun raunuka.

Lamarin ya faru ne a titin First East Circular da ke Benin City a yayin da masu zanga-zangar suke kokarin hura wuta a tsakiyar titin a yammacin Asabar.

An gano cewa, motar kirar SUV tana tahowa ne daga titin Benin zuwa Sapele kuma ta tunkaro titin Sakponba da ke kusa da titin First East Circular yayin da lamarin ya faru.

Matar daya daga cikin wadanda lamarin ya ritsa da su ta ce mijinta ya kirata a kan cewa yana kan hanyar tafiya gida amma cunkoson ababen hawa ya rikesa a titin Sapkonba.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Edo, DSP Chidi Nwabuzor bai samu tofa albarkacin bakinsa ba domin ba a samesa a wayar da aka dinga nemansa ba.

Amma kuma, yayin rubuta wannan rahoton, matasa suna ta barna tare da lalata ababen hawa da kayayyakin gwamnati da ke kan titin Agbor.

KU KARANTA: PDP ta lallasa APC, ta yi nasarar lashe zabukan kananan hukumomi a Bauchi

EndSARS: Mota kirar SUV ta mitsike masu zanga-zanga 4 a kan titi
EndSARS: Mota kirar SUV ta mitsike masu zanga-zanga 4 a kan titi. Hoto daga @Dailytrust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Sirrin da Awolowo ya sanar da ni game da Babangida - Orji Kalu

A wani labari na daban, Gwamnatin tarayya ta ja kunnen masu zanga-zangar dakatar da SARS. Ministan labarai, Lai Mohammed ya fadi hakan a ranar Asabar, 17 ga watan Oktoba.

Mohammed ya ce gwamnatin tarayya ba za ta lamunci tada zaune tsaye ba a kasar nan. Bayan zanga-zangar lumana wadda matasa suka yi akan SARS, gwamnatin tarayya ta ja kunnen jama'a, inda tace sam ba za ta yarda da tayar da tarzoma ba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda Gwamnatin tarayya ta nuna fushinta akan zanga-zangar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel