Daliban Najeriya sun bayyana ranar da za su yi zanga-zanga a NASS

Daliban Najeriya sun bayyana ranar da za su yi zanga-zanga a NASS

- Kungiyar daliban jami'o'i ta kasa ta ce za ta fita zanga-zanga har majalisar dattawa

- Kungiyar tace tabbas dalibai sun yi hakuri da gwamnati kuma hakurinta ya kare

- Kamar yadda wasikar ta bayyana, a ranar Talata za su je har gaban majalisar zanga-zanga

Daliban jami'o'i karkashin inuwar kungiyar daliban jami'o'i ta kasa ta ce hakurinsu ya kare sakamakon dogon yajin aikin da kungiyar malamai masu koyarwa na jami'o'i suka fada.

Daliban sun ce za su nuna rashin jin dadinsu a kan yadda yajin aikin ke tsawaita a ranar Talata.

Sun ce za su fara zanga-zangar ne ta gaban katafaren ginin majalisar tarayya sannan su wuce zuwa ofishin ma'aikatar ilimi daga nan su garzarya zuwa ma'aikatar kwadago da aikin yi.

A wasikar da suka fitar a ranar 13 ga watan Oktoban 2020 wacce suka mika ga majalaisar, kungiyar da ta hada da shugabanninta daga dukkan jami'o'i, ta ce dalibai sun zaunu a gida kuma suna bukatar a janye yajin aikin da gaggawa.

Wasikar ta samu sa hannun shugaban NAUS Ibrahim Lawal, mataimakinsa, Asiwaju Ajibowu da magatakarda, Gbande Abraham.

A yayin zantawa da manema labarai a kan zanga-zangar da ke zuwa, Lawal ya ce gwamnatin ta gaza kuma ya zama dole su yi abinda ya dace saboda tsawaitar yajin aikin.

Ya ce, "Muna gayyatar dukkan dalibai da su fito domin zanga-zanga saboda mun gaji da zaman gida kuma ilimi yana da matukar amfani.

"A watan Augusta, mun rubuta wasika ga ministan ilimi a kan bude makarantu. Mun bakacesa da ya kawo karashe yajin aikin ASUU.

"Amma kuma ministan bai yi martani a kan wasikar ba. Mun yi iyakar hakurin da za mu iya amma bamu ji daga minsitan ba. Mun gaji."

KU KARANTA: Kada ku sa mu yadda cewa wadanda aka lallasa a zaben 2019 ne suka bullo da EndSARS - Hadimin Buhari ga dan Atiku

Daliban Najeriya sun bayyana ranar da za su yi zanga-zanga a NASS
Daliban Najeriya sun bayyana ranar da za su yi zanga-zanga a NASS. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

KU KARANTA: Rashin tsaro: Kungiyoyin arewa sun sanar da ranar fara zanga-zanga maras tsayawa

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya sa hannu akan dokar jihar, wadda ta mayar da Sarkin Kano ya zama shugaba na dindindin ga majalisar sarakunan jihar.

Kafin a gyara dokar ta amince da karba-karbar shugabancin a tsakanin 'yan majalisar 5 na jihar a lokacin da tubabben Sarki Muhammadu Sanusi II yana sarautar Kano.

Sakataren yada labarai na gwamnan, Abba Anwar, a wata takarda yace, "Bayan sa hannu a wannan dokar, Aminu Ado Bayero ya zama shugaban majalisar sarakuna, sannan Gidan Shettima ya zama ofishin majalisar, wanda ba shi da nisa daga fadar sarkin."

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel