Tinubu ya yi magana a kan zarginsa da ake da daukar nauyin zanga-zangar EndSARS

Tinubu ya yi magana a kan zarginsa da ake da daukar nauyin zanga-zangar EndSARS

- Mai magana da yawun Bola Tinubu, Tunde Rahman, ya yi magana a kan zargin da ake wa ubangidansa

- Ana rade-radin cewa Bola Tinubu, jigo a jam'iyyar APC ne yake daukar nauyin masu zanga-zangar EndSARS a Najeriya

- Ya bayyana cewa babu yadda za a yi ubangidansa ya dauka wannan alhakin wanda zai iya kawo manyan kalbale a kasar nan

Tunde Rahman, mai magana da yawun Bola Tinubu, shugaban jam'iyyar APC, yace babu gaskiya a zantukan da ke yawo na cewa yana daga cikin wadanda suka dauka nauyin zanga-zangar EndSARS.

A wata takarda da ya fitar a ranar Asabar, Rahman ya ce Tinubu ba zai iya daukar nauyin zanga-zangar da za ta shafi tattalin arzikin jihar Legas ba.

Ya kara da cewa, ba zai yuwu jigo a jam'iyyar APC ya dauka nauyin zanga-zangar ba a duk jihohin da take faruwa.

"Akwai bukatar a yi bayani tare da gane cewa wannan labarin bogi ne wanda wasu suka kirkiro," Rahman yace.

"Asiwaju Tinubu ba zai iya daukar nauyin zanga-zangar da za ta rufe hanyar shiga da ficen jihar Legas ba.

"Abu na biyu shine Asiwaju Tinubu ya yadda cewa 'yan Najeriya suna da damar zanga-zanga ta lumana tare da bayyana ra'ayinsu. Masu zanga-zangar suna mika bukatar su wanda gwamnati ke dubawa.

"Kamar sauran 'yan Najeriya, Bola Tinubu ya yadda cewa bai dace 'yan sanda su dinga cin zarafin jama'a ba.

"Ya yadda cewa lokaci yayi da matasa za su samu damar tattaunawa tare da samun abinda suke so daga gwamnati. Wadanda suka dauka nauyin wannan labarin sun kirkiri bogi ne kawai." yace.

KU KARANTA: Dan sandan da ya jagoranci kafa rundunar SARS ya yi nadama

Tinubu ya yi magana a kan zarginsa da ake da daukar nauyin zanga-zangar EndSARS
Tinubu ya yi magana a kan zarginsa da ake da daukar nauyin zanga-zangar EndSARS. Hoto daga @ChannelTV
Asali: Twitter

KU KARANTA: Gide, shugaban 'yan bindigar Zamfara ya bada sharadin ajiye makamansa

A wani labari na daban, rundunar Sojin Najeriya tace a shirye take ta kare Najeriya da damokaradiyyarta komai rintsi.

A wata takardar ranar Laraba, Sagir Musa, mukaddashin kakakin rundunar sojin Najeriya ya ja kunnen masu tada tarzoma da su kiyaye yin duk wani abu da zai cutar da kasar nan.

A ranar Talata ne wani bidiyon wasu sojoji dake cin zarafin wani mai daukar hoton gidan talabijin din ARISE, har da kwace masa kayan aiki a lokacin da yake daukar Bidiyon masu zanga-zanga a majalisar dattawa yayi ta yawo a kafafen sada zumuntar zamani.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel