2023: Ibo na yaudarar kansu a kan shugabanci - Shugabannin arewa sun yi martani mai zafi

2023: Ibo na yaudarar kansu a kan shugabanci - Shugabannin arewa sun yi martani mai zafi

- Shugaban 'yan arewa a yankin Kudu, Alhaji Musa Saidu ya yi magana a kan shugabancin kasa na 'yan kabilar Ibo

- Ya tabbatar da cewa duk wanda ke yi wa Ibo alkawarin shugabancin kasa kawai yana yaudararu su ne

- Kamar yadda yace, 'yan arewa suna da babbar muhimmiyar rawar takawa wurin ganin nasarar kowanne mutum hayewa shugabancin kasa

Shugaban arewa a Kudu, Alhaji Musa Saidu, ya bukaci 'yan kabilar Ibo da su manta da batun shugabancin kasa a 2023 idan suka kasa tabbatar da zaman lafiya a fadin kasar nan.

A wata tattaunawa da Saidu yayi da Vanguard, ya ce masu yi wa 'yan kabilar Ibo alkawarin shugabancin kasa babu bukatar su cike gibin rashin zaman lafiya da ya mamayesu suna yaudararsu ne kawai.

Ya ce a lokuta marasa adadi kungiyoyin Ibo suna kashe 'yan arewa masu tarin yawa a yankin su kuma babu wani shugabansu da ya taba kushe hakan.

"Duk wanda ya yi alkawarin shugabancin kasa a 2023 ga 'yan kabilar Ibo yana yaudararsu ne kawai. 'Ya'yanku suna kashe Hausawa a Ribas. Idan sun so, su je gaban Buhari ko Asiwaju Tinubu, ba za su samu komai ba matukar basu tabbatar da zaman lafiya ba," yace.

Saidu wanda shine ke da sarautar Dam-buran Fatakwal kuma shugaban 'yan arewa mazauna jihar Ribas, ya ce yana son yankin Neja Delta kuma ba zai ki ba idan dan kabilar Ijaw, Urhobo, Itsekiri ko wata kabila ta yankin ta kawo dan takara.

Ya kara da cewa, shi mataimaki na musamman ne ga shugaban yankin Neja Delta, Chief Harold Dappa Biriye, na tsawon shekaru 25 kuma yana kaunar yankin.

Ya ce akwai bukatar su sani cewa, 'yan arewa ne ke da karfin yawan kuri'un da za su iya bayyana wanda suke so ya shugabanci kasa kuma a amince.

KU KARANTA: Gide, shugaban 'yan bindigar Zamfara ya bada sharadin ajiye makamansa

2023: Ibo na yaudarar kansu a kan shugabanci - Shugabannin arewa sun yi martani mai zafi
2023: Ibo na yaudarar kansu a kan shugabanci - Shugabannin arewa sun yi martani mai zafi. Hoto daga Vanguardngr.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Dan sandan da ya jagoranci kafa rundunar SARS ya yi nadama

A wani labari na daban, rundunar Sojin Najeriya tace a shirye take ta kare Najeriya da damokaradiyyarta komai rintsi.

A wata takardar ranar Laraba, Sagir Musa, mukaddashin kakakin rundunar sojin Najeriya ya ja kunnen masu tada tarzoma da su kiyaye yin duk wani abu da zai cutar da kasar nan.

A ranar Talata ne wani bidiyon wasu sojoji dake cin zarafin wani mai daukar hoton gidan talabijin din ARISE, har da kwace masa kayan aiki a lokacin da yake daukar Bidiyon masu zanga-zanga a majalisar dattawa yayi ta yawo a kafafen sada zumuntar zamani.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel