Daga karshe Oyetola ya yi martani kan harin da aka kai masa, ya ce an turo yan daban ne domin su kashe shi

Daga karshe Oyetola ya yi martani kan harin da aka kai masa, ya ce an turo yan daban ne domin su kashe shi

- Gwamna Oyetola na jihar Osun ya bayyana cewa yan daban da suka kai ma ayarin motarsa hari sun so kashe shi ne

- An kai wa Oyetola da wasu yan majalisarsa hari a ranar Asabar, 17 ga watan Oktoba, a garin Osogbo

- Gwamnan a ranar Lahadi, 18 ga watan Oktoba, ya bayyana lamarin a matsayin abun bakin ciki

Kimanin sa’o’i goma bayan wasu masu zanga-zangar kawo karshen SARS sun kai masa hari tare da mataimakinsa, Gwamna Adegboyega Oyetola na jihar Osun ya bayyana cewa wasu yan daba ne suka aiwatar da lamarin.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Oyetola, mataimakinsa Benedict Alabi da sauran yan majalisar zartarwa ta jihar sun tsallake rijiya da baya a ranar Asabar, 17 ga watan Oktoba, lokacin da wasu yan daba suka kai masu hari bayan yin jawabi ga masu zanga-zangar.

Legit.ng ta tattaro cewa a yayinda yake jawabi na fadin jihar a safiyar ranar Lahadi, 18 ga watan Oktoba, gwamnan ya bayyana lamarin a matsayin abun bakin ciki.

Daga karshe Oyetola ya yi martani kan harin da aka kai masa, ya ce an turo yan daban ne domin su kashe shi
Daga karshe Oyetola ya yi martani kan harin da aka kai masa, ya ce an turo yan daban ne domin su kashe shi Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

Ya ce ya shiga sahun masu zanga-zangar #EndSARS ta hanyar yin tattaki daga Alekuwodo domin haduwa da masu zanga-zangar a mararrabar Ola-Iya inda ya yi masu jawabi.

KU KARANTA KUMA: Bidiyon wani mai bayar da hannu a titi da masu zanga-zanga suka karrama saboda kwazonsa

Gwamna Oyetola ya ce:

“Sai dai kuma yan daba sun mamaye wajen zanga-zangar domin su kashe ni. Mun tsere daga wajen ba tare da harba masu bidiga ko bada masu barkonon tsohuwa ba.

“Amma bayan al’amarin, mun tattaro cewa mutane biyu sun mutu. Daya daga cikinsu ya rasu sakamakon hatsarin babur.”

Ya ce harin na da nasaba da siyasa sannan an so kashe shi da sauran mambobin majalisar zartarwa na jihar ne.

KU KARANTA KUMA: Lawan ya dauki nauyin aurar da marayu da marasa gata su 100 a Yobe

A gefe guda, Funke Egbemode, kwamishinan watsa labarai na jihar Osun, ta ce harin da aka kai wa gwamnan jihar Gboyega Oyetola a wurin zanga-zangar #EndSARS a Osogbo, babban birnin jihar, yunkuri ne na neman kashe shi.

Idan za ku tuna dai ana gudanar da zanga-zanga a fadin kasar kan neman a soke rundunar SARS sakamakon zarginsu da ake yi da cin zarafin al’umma.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel