Yunƙurin juyin mulki aka yi wa gwamnan Osun - Kwamishina

Yunƙurin juyin mulki aka yi wa gwamnan Osun - Kwamishina

- Kwamishinan watsa labarai na jihar Osun, Funke Egbemode ta ce harin da aka kai wa gwamnan jihar, Gboyega Oyetola yunkurin juyin mulki ne

- Gwamna Oyetola yana cikin yi wa masu zanga-zangar #EndSARS jawabi ne a Osogbo kwatsam wasu 'yan daba suka kai musu hari

- 'Yan daban sun halaka mutum guda tare da jikkata wasu da dama cikin masu zanga-zangar kana sun kai wa motar ayarin gwamnan hari

Funke Egbemode, kwamishinan watsa labarai na jihar Osun, ta ce harin da aka kai wa gwamnan jihar Gboyega Oyetola a wurin zanga-zangar #EndSARS a Osogbo, babban birnin jihar, yunkuri ne na neman kashe shi.

Oyetola yana tsaka da yi wa masu zanga-zangar jawabi a mahaɗar Olaiya a Osogbo, babban birnin jihar, inda wasu da ake zargin ƴan-daba ne suka ƙaddamar da hari a kan taron jama'ar.

Yunƙurin juyin mulki akayi wa gwamnan Osun - Kwamishina
Motar tawagar Gwamna Oyetola. Hoto daga @thecableng
Asali: Twitter

An kashe mutum ɗaya yayin da wasu da yawa suka jikkata yayin harin.

An lalata mototoci guda biyu daga cikin ayarin motocin gwamnan.

DUBA WANNAN: Kotu ta raba auren shekara 18 saboda mata ba ta gamsar da mijinta

Yayin da ta ke maida martani, Egbemode,wadda ya kasance a inda aka aikata harin,yace harin yafi ƙarfin zanga-zangar kawo karshen sashe na musamman mai yaƙi da fashi da makami na rundunar ƴan sanda (#EndSARS).

Waɗanda suka kawo harin ba masu zanga-zangar ba ne.

Ta bayyana takaici yadda masu kai harin suka fake a cikin masu zangar-zangar lumana don cimma mummunar manufarsu.

"Yunƙuri ne na kisan kai.Haƙiƙa wannan ya zarce zanga-zangar kawo ƙarshen sashen yaƙi da fashi da makami (#EndSARS).

KU KARANTA: Wani da ake zargi dalilin bindigu ne ya mutu yayin yunkurin tsere wa hukuma a Katsina

Mutanen da suka ƙaddamar da harin ba masu zanga-zangar ba ne kwata-kwata," a cewarta.

"A ɗau kwanaki ana gudanar da zanga-zangar ,kuma ba'a taɓa kaiwa wani jami'in gwamnati hari ba.

Sai dai,harin da aka kai yau yasa labarin ya sha ban-ban.Bawai ƙoƙari ne kara zube ba.Maharan sun gama tsara komai.

Suna ɗauke da bindigu da sauran muggan makamai.

A wani labarin daban, gwamnatin tarayyar Najeriya ta umurci ma'aikatan gwamnati da ke aiki daga gida tun watan Maris saboda korona su koma aiki ranar Litinin 19 ga watan Oktoba.

Shugaban kwamitin Shugaban Ƙasa ta Yaƙi da Korona, PTF, Boss Mustapha da jagora na ƙasa, Sani Aliyu ne suka sanar da haka yayin taron manema labarai ranar Talata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel