A kan tattaro min takardun neman aiki a kalla 200 duk lokacin da na tafi ziyarar aiki - Pantami

A kan tattaro min takardun neman aiki a kalla 200 duk lokacin da na tafi ziyarar aiki - Pantami

- Ministan sadarwa ta tattalin arziki na zamani, Isa Pantami ya ce ana bashi takardun neman aiki a kalla 200 duk lokacin da ya kai ziyarar aiki jihohi

- Dakta Pantami ya shawarci matasan su mayar da hankali wurin koyon sana'o'i da kirkire-kirkire a maimakon dogaro da takardun karatun zalla

- Ministan ya ce a kasashen da suka cigaba akan bawa masu shaidar karatu karami a wajen rabon aiki yayin da masu kirkire-kirkire da sana'o'i ke samun kaso mafi rinjaye

Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr Isah Ali Pantami, ya bayyana cewa dole ne matasan Najeriya su maida hankali wajen koyon sana'a kuma su dena dogora ta shaidan kamalla karatu zalla.

Kamar yadda ya bayyana, 'yan Najeriya sunfi maida hankali ga samun shaida ta karatu fiye da koyon sana'o'i, ya kuma kara da cewa akwai sana'o'i da dama a kasar nan sai dai kuma rashin maida hankali a koyi sana'o'in ya sanya ba a cike guraben ba.

Ina samun takardun neman aiki 200 duk lokacin da nake yanki na - Pantami
Dakta Isa Pantami. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

Ya ce, "Wasu lokutan idan kaje kaddamar da wani aikin, duk wanda ka kaiwa ziyara zai dauko maka tulin takurdun neman aiki".

DUBA WANNAN: Kotu ta raba auren shekara 18 saboda mata ba ta gamsar da mijinta

A duk jihar dana kai ziyara nakan dawo da takurdun neman aiki fiye da 200; wannan abun dubawa ne kwarai. Kasashe da suka ci gaba, matasansu basa son yin aiki a karkashin gwamnati sai dai aikin sa kai.

Idan aka samu horon sana'a ko daga muhallinmu zamu samu damar rage zaman banza, a bangaren mu kuma muna iya bakin kokarin mu wajen ganin mun kawo cigaba a fannin kirkira da koyar da sana'o'i.

Pantami ya bayyana haka ranar Juma'a, a wajen kaddamar da cibiyar kimiyya da fasaha a jami'ar jihar Gombe, wadda hukumar kula da cigaban kimiyya da fasaha ta kasa (NITDA) ta gina.

KU KARANTA: Wani da ake zargi dalilin bindigu ne ya mutu yayin yunkurin tsere wa hukuma a Katsina

Ministan ya ce, "a kasashen da suka cigaba akan bawa masu shaidar karatu kaso mafi kankanta a wajen rabon aiki yayin da masu kirkire-kirkire da sana'o'i ke samun kaso mafi rinjaye.

"Shaidar takarda kamata yayi ace abune da yake tabbatar da cewa kana da fasahar kirkira ko shaidar ka kware a wata sana'a. Fasaha itace take aikin bawai shaidar takarda ba".

A Najeriya, matsalar da muke fama da ita kenan.

Ina ta kokarin ganin na haɗa kai da 'yan uwana na majalisar zartarwar fadar shugaban kasa wajen ganin mun haɗa hannu don tabbatar da cewa ana koyon sana'o'i, ya kamata mu rage dogaro da takarda mu kuma maida hankali wajen kirkira da sana'o'i."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel