Da duminsa: 'Yan daba sun kaiwa tawagar gwamnan APC hari (Hotuna da bidiyo)

Da duminsa: 'Yan daba sun kaiwa tawagar gwamnan APC hari (Hotuna da bidiyo)

- Hankula sun tashi a shataletalen Ola-Iya da ke birnin Osogbo, babban birnin jihar Osun

- Wasu 'yan daba sun kai wa Gwamna Gboyega Oyetola hari inda suka dinga jifan tawagarsa

- Gwamnan ya kammala jawabi ga masu zanga-zangar EndSARS yayin da 'yan daban suka kai masa hari

Rikici ya barke a fitaccen wurin nan na shataletalen Ola-Iya da ke Osogbo, babban birnin jihar Osun yayin da wasu 'yan daba suka kai wa tawagar Gwamna Gboyega Oyetola hari.

'Yan daban sun jefe tawagar gwamnan da duwatsu, adduna tare da sanduna bayan ya kammala jawabi ga masu zanga-zangar EndSARS a babban birnin jihar.

Gwamnan ya yi tattaki tare da wasu 'yan majalisar jihar daga yankin Alekuwodo zuwa inda masu zanga-zangar suke a Ola-Iya.

Bayan kammala jawabinsa, Gwamnan ya juya ya bar wurin amma kafin kace mene sai 'yan daban suka fara jifansa.

Babban mai bai wa gwamnan shawara ta musamman a kan harkar yada labarai, Mabel Aderonke, ta tabbatar da aukuwar lamarin ga jaridar The Nation.

Ta ce Gwamnan ya kammala jawabi ga masu zanga-zangar EndSARS, amma kafin ya bar wurin wasu 'yan daba sun mamaye wurin inda suka dinga jifan tawagarsa.

Da duminsa: 'Yan daba sun kaiwa tawagar gwamnan APC hari (Hotuna da bidiyo)
Da duminsa: 'Yan daba sun kaiwa tawagar gwamnan APC hari (Hotuna da bidiyo). Hoto daga @BBCHausa
Asali: Twitter

KU KARANTA: Matashi mai digiri ya adana kwalinsa, ya fada harkar noma kuma yana samun nasarori

Da duminsa: 'Yan daba sun kaiwa tawagar gwamna hari (Hotuna da bidiyo)
Da duminsa: 'Yan daba sun kaiwa tawagar gwamna hari (Hotuna da bidiyo). Hoto daga @BBCHausa
Asali: Twitter

Da duminsa: 'Yan daba sun kaiwa tawagar gwamna hari (Hotuna da bidiyo)
Da duminsa: 'Yan daba sun kaiwa tawagar gwamna hari (Hotuna da bidiyo). Hoto daga @BBCHausa
Asali: Twitter

KU KARANTA: Matar aure ta gurfana gaban kotu bayan ta soka wa makwabciya wuka a kai

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong ya yabi majalisar dinkin duniya akan kokarinta wurin kawo zaman lafiya a Najeriya, musamman a arewa maso gabas.

Yace hakika shigar majalisar cikin al’amarin ya haifar da 'da mai ido. Yace jihar Filato tana fuskantar matsalar rashin tsaro amma tun bayan majalisar ta sa baki al’amura suka fara daidaita.

Gwamnan yace, “A tarihi, jiharmu ce jihar farko da kungiyar ta fara samar wa zaman lafiya.”

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel