Kwana hudu bayan harbinsa, babban dan siyasa a Kogi, Adejo, ya mutu

Kwana hudu bayan harbinsa, babban dan siyasa a Kogi, Adejo, ya mutu

- Jihar Kogi ta yi rashin daya daga cikin manyan yan siyasarta, Adejo Akowe

- Akowe ya mutu ranar Asabar, 17 ga Oktoba, a asibitin kasa dake Abuja

- Tsohon shugaban karamar hukumar Dekinan ya mutu ne kwanaki hudu bayan harbinsa da akayi

Jihar Kogi ta yi rashin tsohon shugaban karamar hukumar Dekina, Adejo Akowe, a ranar Asabar 17 ga Oktoba, 2018.

Akowe, a cewar The Nation, ya mutu sakamakon raunukan harsasai da ya sha bayan wasu yan bindiga suka kai masa hari a Anyingba ranar Talata, 13 ga Oktoba.

Tsohon shugaban karamar hukumarn ya mutu ne da safiya Asabar a asibitin kasa dake Abuja.

Gabanin mutuwarsa, an yi kokarin kashe Akowe lokacin zaben gwamnan jihar a shekarar 2015.

DUBA NAN: Sabbin mutane 212 sun kamu da Korona a Najeriya, jimilla 61,194

Kwana hudu bayan harbinsa, babban dan siyasa a Kogi, Adejo, ya mutu
Kwana hudu bayan harbinsa, babban dan siyasa a Kogi, Adejo, ya mutu. Hoton daga The Nation
Asali: UGC

KU KARANTA: Hukuncin zanga-zanga a Shariah - Dr. Ahmad Mahmud Gumi

A wani labarin, wata tankar dakon man fetur ta kama da wuta cikin dare a kan gadar Otedola da ke jihar Legas.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne cikin dare misalin karfe (3) uku.

Babu rahoton cewa an rasa rai sakamakon gobarar da tankar ta yi a lokacin da aka hada wannan rahoton.

Mai magana da yawun hukumar kai agajin gaggawa na jihar Legas, LASEMA, Nosa Okunbor ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel