Sabbin mutane 212 sun kamu da Korona a Najeriya, jimilla 61,194

Sabbin mutane 212 sun kamu da Korona a Najeriya, jimilla 61,194

- Kamar yadda ta saba, hukumar NCDC ta saki adadin yan Najeriya da suka kamu da cutar Korona

- Yayinda ake smaun raguwar masu kamuwa a Najeriya, abubuwa na munana a kasar Ingila

- Har yanzu kasar Rasha kadai ce ta sanar samun rigakafin cutar har guda biyu

Hukumar hana Yaduwar Cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa annobar cutar COVID-19 ta sake harbin sabbin mutane 212 a fadin Najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:15 na daren ranar Juma'a 16 ga watan Oktoba, shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta fitar, ta ce mutanen 212 sun fito daga jihohin Najeriya kamar haka:

Lagos-85

Oyo-72

FCT-21

Ogun-11

Plateau-11

Katsina-6

Kaduna-5

Osun-1

Kawo yanzu a duk fadin Najeriya, cutar ta harbi mutum 61,194 sai kuma mutum 52,304 da aka sallama daga cibiyoyin killace masu cutar bayan samun waraka, yayin da mutum 1119 suka riga mu gidan gaskiya.

DUBA NAN:Rundunar Mayakan sama sun yiwa yan bindiga ruwan wuta a Borno (Bidiyo)

Sabbin mutane 212 sun kamu da Korona a Najeriya, jimilla 61,194
Sabbin mutane 212 sun kamu da Korona a Najeriya, jimilla 61,194 Hoto: @NCDC
Asali: Twitter

Kun ji cewa cewa dalibai da malaman wata makaranta mai zaman kanta dake unguwar Lekki, a jihar Legas sun kamu da mugun cutar Korona.

Legit.ng ta tattaro cewa kwamishanan lafiyan Legas, Akin Abayomi, ya ce an gano sun kamu da cutar ne bayan binciken da aka gudanar a makarantar.

KARANTA: Bidiyon jami'in dan sanda rike da bindiga yana nadin tabar wiwi ya bayyana

Kwamishanan yayinda yake bayanin binciken, ya ce wata daliba mai shekara 14, yar ajin SS1 ta fara lafiya ranar 3 ga Oktoba kuma aka tura ta gida bayan karamin jinyar da tayi a makarantan.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel