Tanka ta kama da wuta a gadar Otedola da ke Legas

Tanka ta kama da wuta a gadar Otedola da ke Legas

- An sake samun afkuwar gobarar tankar dakon man fetur a gadar Otedola a jihar Legas

- Wata babban mota dauke da yadi ne ta yi karo da tankar man fetur hakan yasa dukkansu suka kone

- Hukumar kai agajin gaggawa ta Legas, LASEMA, ta tabbatar da afkuwar gobarar

Wata tankar dakon man fetur ta kama da wuta cikin dare a kan gadar Otedola da ke jihar Legas.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne cikin dare misalin karfe (3) uku.

Babu rahoton cewa an rasa rai sakamakon gobarar da tankar ta yi a lokacin da aka hada wannan rahoton.

Tanka ta kama da wuta a gadar Otedola da ke Legas
Tanka ta kama da wuta a gadar Otedola da ke Legas. Hoto daga @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Kotu ta raba auren shekara 18 saboda mata ba ta gamsar da mijinta

Mai magana da yawun hukumar kai agajin gaggawa na jihar Legas, LASEMA, Nosa Okunbor ya tabbatar da afkuwar lamarin.

KU KARANTA: Dalibi dan shekara 20 ya auri mata biyu cikin wata daya (Hotuna)

A cikin sanarwar, Okunbor ya bayyana cewa lamarin ya faru ne yayin da wani trela dauke da yadi ta yi karo da tanka dauke da man fetur.

Motoccin biyu sun kama da wuta amma babu wanda ya mutu.

"Ba a rasa rai ba. Jami'an hukumar LASEMA da jami'an kwana-kwana sun kashe wutan.

"Mun gama kashe gobarar," in ji shi.

A wani labarin daban, mutum tara ne suka riga mu gidan gaskiya yayin da wasu uku suka jikkata sakamakon mummunan hatsarin mota da ya faru a Kano kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Zubairu Mato, Kwamandan Hukumar Kiyayye Hadurra ta Kasa, FRSC, a jihar cikin wata sanarwa da ya ce hatsarin ya faru ne misalin karfe 9 na safe da ya ritsa da mota da adaidaita sahu a hanyar Kano zuwa Zaria a kauyen Imawa da ke karamar hukumar Kura.

Kwamandan ya ce hatsarin ya ritsa da trela mai lamba KMC158XW, wata karamar mota mai lama AE 884 GZW da adaidaita sahu mara lamba.

Ya ce trelan da motar sun yi karo ne a kokarin su na kaucewa adaidaita sahun da ke taho wa daga ta dayan bangaren titin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164