Wani da ake zargi dalilin bindigu ne ya mutu yayin yunkurin tsere wa hukuma a Katsina

Wani da ake zargi dalilin bindigu ne ya mutu yayin yunkurin tsere wa hukuma a Katsina

- Wani da ake zargi mai sayar wa 'yan bindiga makamai ne ya mutu a karamar hukumar Safana a Katsina

- Jami'an tsaro sun tsayar da shi a lokacin da suka gan shi a babur zai nufi cikin daji amma sai ya ki tsayawa

- Jami'an tsaron sun harbe shi a kafa yayin da ya ke yunkurin guduwa kuma an gano harsasai a karkashin siddin babur dinsa daga bisani

Wani da ake zargi dalilin bindigu ne ya mutu yayin yunkurin tserewa daga hannun hukuma a Katsina
Rundunar 'yan sandan Najeriya. Hoto daga @MobilePunch
Asali: UGC

Wani mutum mai shekaru 35, Abubakar Haruna da ake zargin mai garkuwa ne kuma mai sayar wa 'yan bindiga makamai ya mutu sakamakon raunin harsashi yayin da ya yi yunkurin tserewa jami'an tsaro a ranar Laraba.

A cewar 'yan sanda, an harbi Haruna dan asalin kauyen Ilela a karamar hukumar Safana a kafarsa a mahadar Tsaskiya da ke karamar hukumar ta Safana.

DUBA WANNAN: Dalibi dan shekara 20 ya auri mata biyu cikin wata daya (Hotuna)

An ce yana dauke da harsashi masu tsawon 7.62mm na bindigar AK 47 guda 600 zai tafi dajin Rugu ya kai wa 'yan bindiga ne 'yan sanda da 'yan banga suka kama shi.

Ya boye harsashin cikin wani buhu da ke karkashin siddin babur din da ya ke tukawa.

KU KARANTA: Kotu ta raba auren shekara 18 saboda mata ba ta gamsar da mijinta

Kakakin 'yan sandan jihar, Gambo Isah ya ce, "An kama bata garin a Tsaskiya junction yana tuka wata babur kirar Bajaj mara rajista zai shiga daji.

"Wanda ake zargin ya ki tsayawa a lokacin da aka bukaci ya tsaya, hakan yasa aka harbe shi a kafa."

An yi holen gawar Haruna a hedkwatan rundunar 'yan sanda na jihar Katsina a yammacin ranar Alhamis.

A wani labarin daban. wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Jos ta tsare wani ma'aikacin gidan gyaran hali mai suna Danladi Bako bisa zargin mallakar wani abu da ake zargin tabar wiwi ce.

Mallakar tabar wiwi laifi ne da aka tanadarwa hukunci a sashe na 19 na dokar hukumar NDLEA.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel